Kaduna za ta dawo mai jam’iyya ɗaya – Uba Sani

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Kaduna ya ce jam’iyyar APC za ta cigaba da mamaye jihar Kaduna har sai ta kawo jam’iyyar ɗaya ce a jihar.

Ya ce a halin yanzu akwai ‘yan majalisun wakilai 4 da wasu ‘yan majalisun dokokin jihar daga ɓangarori daban-daban da suka dawo APC daga jam’iyyar adawa.

Gwamna Uba Sani ya yi waɗannan kalamai ne a ranar Litinin a Zariya wanda ya ce sauyin sheƙar wasu ‘yan jam’iyyar adawa zuwa APC, “kyakkyawar alama ce ta irin ayyukan alkhairi da muke yi da tafiya da kowa da kowa a jihar Kaduna.”

Shugaban majalisar dattawa, Tajudeen Abbas, ya raba ababen hawa 117ds suka haɗa da: motocin Hiluɗ guda 20 motocin ɗaukar marasa lafiya guda 2 da motocin bas masu cin mutane 18 guda 2 da motoci ƙirar Golf, Corolla da Peugeot 406 da babur mai ƙafa uku 200 da aka fi sani da Keke Napep da babura 1,000 – waɗanda aka raba wa mutane daban-daban.

A yayin da yake magana a wurin taron, gwamnan jihar ya yaba wa kakakin majalisar wakilai yana mai cewa jihar Kaduna da ƙasa bakiɗaya na alfahari da irin yadda yake hidimta wa Nijeriya. Ga kuma ayyuka da ya samo wa jihar.

Uba Sani ya ce tun da Abbas ya zama kakaki, “ya yi ƙoƙarin kawo ayyukan gina rayuwar al’umma a garin Zariya da sauran sassan jihar kuma ina murna da wannan abu.”

A cewarsa Abbas ya kawo cigaba a ɓangaren ilimi da lafiya da noma da ya haɗa da samar da kayan bunƙasa rayuwa a jihar Kaduna.

Ya ce ba kaɗai ya mai da hankali ne ga mazaɓarsa ta Zariya ba, ayyukansa sun tallafa wa hatta waɗanda suke sauran mazaɓu musamman yankin Kaduna ta Arewa.

“A yau mun ga irin nasarorin da mai girma kakaki ya kawo wa al’umma da ya raba musu. Kuma ba iya mazaɓarsa ce ba ta Zariya, har ma da sauran ƙananan hukumomin da ke shiyya ta 1 waɗanda suka amfana da wannan tallafi.”

“Yana aiki sosai da wannan gwamnatin ta yadda shi ba wai kawai ginshiƙi ba ne na jihar Kaduna, shi ginshiƙi ne ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu. Na haɗu da shugaban ƙasa kuma ya faɗa min cewa yana jin daɗin yadda mai girma kakaki ke gudanar da ayyukansa a majalisa. Kuma mu ma da muka taɓa shiga majalisa, muna alfahari da irin ayyukan da yake yi na wakilci.”

“Duk masu gutsuri tsoma kan kakaki, bari na shaida muku cewa, da yardar Allah sai kakaki ya kafa tarihi na zama shugaban majalisar wakilai karo na biyu kuma za mu cigaba da inganta jihar Kaduna. Abin da muka sa a gaba shi ne cigaban Kaduna,” inji Uba Sani.

A yayin da yake jawabi, kakakin majalisar wakilai, Abbas, ya gode wa ‘yan mazaɓarsa saboda irin gudunmuwar da suke ba shi, inda ya ba su tabbacin cigaba da yin ƙoƙari wajen samo ayyukan raya al’umma.

A yayin da yake magana game da zamansa kakakin majalisa, Abbas Tajudeen, ya ce shugaba Tinubu ne na ɗaya wajen tallafa masa duk da bai shi, shi da shi ba.

“Shugaban ƙasa ya ban goyon baya ta la’akari da abin da ya karanta ya kuma ji a kaina. Bai taɓa haɗuwa da ni ba, amma a haka ya taimaka min. An tura masa sunaye da yawa amma ya zaɓe ni saboda ya yi amanna da abin da ya karanta game da ni.”

Daga nan ya buƙaci al’ummar mazaɓarsa da su mara wa shugaban ƙasa baya tare da yi masa addu’a.

Sannan ya ce mutum na biyu da ya tallafa masa shi ne gwamnan Kaduna wanda ya yi duk mai yuwuwa wajen ganin ya samu nasara.

”Gwamna Uba Sani ya taimaka min a lokacin da muƙarraban gwamnatin da suka gabata suka ƙi taimakona. Ya mara min baya tun kafin ya shiga ofishinsa kuma ya cika alƙawari.”

Abbas ya yi alƙawarin cewa, “babu wani abu da zai shiga tsakaninsa da gwamnan jihar” a yayin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar.

“Ko da zan zama mutum na ƙarshe da ke tsaye a bayan Uba Sani zan yi ba zan ja da baya ba.”

“Sai ma a 2027 gwamna Uba Sani zai ga irin goyon bayan da za mu nuna masa. Za mu yi gangami a Zariya da jihar Kaduna bakiɗaya wajen tabbatar da nasararsa,” inji kakakin.

By ukarofi