Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Maiduguri
Ƙungiyar matasan Nijeriya (NYCN), reshen jihar Borno ta nemi gwamnatin jihar ta kafa hukumar da za ta magance tashe-tashen hankula da rashin aikin yi a tsakanin matasan jihar.
Majalisar matasan ta bayyana cewa kusan dukan laifukan da ake aikatawa akwai zargin matasa ne masu aikata su, waɗanda ƙasar nan ke fama da tashe-tashen hankula, ta ƙara da cewa, duk da cewa matasa suna da hannu wajen samar da zaman lafiya a cikin al’umma.
Wannan furucin ya fito ne daga shugaban ƙungiyar NYCN a jihar Borno, Kwamared Tanimu Tahir, a lokacin bikin ranar matasa, wadda Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) ta ware kowace shekara, a Maiduguri ranar Asabar.
“A jiharmu ta Borno, muna da buƙatar samar da hukumar daƙile tsashe-tashen hankula da rashin aikin yi, wanda ta hakan ne za mu yi amfani da shawarwarin hukumar, wajen tsare-tsaren ta masu ɗorewa waɗanda za su iya magance tashe-tashen hankula da rashin aikin yi a tsakanin matasa.”
Ya yi nuni da cewa hukumar za ta taimaka wajen sauƙaƙa tsantsauran ra’ayi da ke tunzura matasa dama a jihar Borno kimanin miliyan 1.5, saɓanin takwarorinsu a Legas da wasu jihohi na ƙasar nan. Ya jaddada cewa matasan jihar su na da hukumar matuƙa.
Ya ce, “wannan hukuma za ta iya kasancewa matakala zuwa ga samun kyakkyawan sauyin rayuwar matasa da nema musu mafita a wajen gwamnatin jihar, tare da alaƙa da sauran abokan haɗin gwiwa don magance matsalolin da matasa ke fuskanta cikin tsanaki.”
Har wala yau kuma, ya ce matasan za su ci gajiya da amfana da muhimman abubuwan da suka dace a ɓangarorin rayuwa daban-daban wajen bunƙasa zaman lafiya don shawo kan ƙaubalen tsaro da ƙarancin abinci da ayyukan yi.
“Muna tattaunawa game da yadda matasa za su kasance masu muhimmanci wajen tsara manufofi tare da ƙawance a matakin tarayya da jihohi.”
