Ranar Matasa 2022: Atiku ya buƙaci ilimi ya zama haƙƙi ga matasan Nijeriya

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Matasan Jam’iyyar PDP sun gudanar da bikin ranar matasa ta duniya 12 ga Agustan 2022 a Abuja, yayin wani ƙayataccen taro da ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar daga sassan ƙasar nan ciki har da ɗan takarar shugabancin ƙasar nan na Jam’iyyar PDP a zaven baɗi Atiku Abubakar da Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa Dr. Iyorchia Ayu da sauran shugabanni.

A jawabinsa na buɗe taron, shugaban matasa na Jam’iyyar ta PDP Prince Muhammad Kadaɗe Sulaiman ya ce manufar taron mai taken: ‘Haɗin gwiwar gudanar da shugabanci tare da mtasa na cikin muradun cigaba mai ɗorewa na Majalisar Dinkin Duniya’. Sa’ilin da kuma ya buƙaci sanya matasa a cikin shugabanci tare da buƙatar ɗora su a hanya da ba su horo.

Shugaban taron Honorabul Ndudi Elumelu ya ce manyan shugabannin jam’iyyar sun halarci taron ne saboda muhimmancin da matasa ke da shi a wurin su, musamman wajen gina ƙasa, Honarabul Elumelu wanda shi ne Shugaban Marasa Rinjaye na majalisar wakilai ya yi tsokaci kan yadda Wazirin Adamawa ke ƙaunar matasa kamar yadda ya nuna a mu’amalar sa da su da kuma yadda yake sanya su a harkokin kasuwancinsa.

Ya kuma jinjinawa Kwamitin Zartarwa na jam’iyyar, inda ya buƙaci matasa su zama masu haɗin kai da tsayawa kan manufa wajen nuna goyon bayansu ga PDP, domin idan Atiku ya zama shugaban ƙasa zai gyara matsalolin da jam’iyyar APC ta ƙirƙire su.

A bayanin da mataimaki na musamman ga Atiku Abubakar kan kafafen yaxa labarai Abdulrasheed Shehu ya fitar, ya ambato ɗan takarar shugabancin Nijeriya na Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, na jinjinawa matasan, saboda jajircewarsu duk kuwa da taɓarɓarewar alamura a ƙasa, inda ya jaddada aniyarsa ta samar da gwamnati mai ƙunshe da matasa, idan aka zaɓe shi, kasancewar yana son ganin ya horar da matasa ya ɗora su akan hanyar shugabanci domin su karɓi ragamar ƙasar da nufin kaita tudun mun tsira.

Ya buƙaci matasan su kansace tsayayyu wajen tallafa wa PDP ta kuvutar da Nijeriya daga mummunan shugabanci.

Ya kuma koka kan yajin aikin Ƙungiyar ASUU wanda ya bar matasa zaune a gida, yana mai cewa ilimi haƙƙi ne ga matasa, wanda bai kamata a yi wasa da shi ba.