DAGA MUKHTAR YAKUBU
Ƙungiyar ƙwararru ta masu shirya fim, MOPPAN reshen Jihar Kano sun yi zama da hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi domin tattauna yadda za a yi tafiya domin wayar da kan al’umma a game da illar sha da kuma fataucin miyagun ƙwayoyi.
Taron wanda ya gudana a ranar Alhamis ɗin da ta gabata an yi shi ne a ofishin ƙungiyar MOPPAN reshen Jihar Kano da ke Kofar Dukawuya kan titin B U K a cikin garin Kano.
Tun da farko da yake jawabi a game da zuwan na su ofishin ƙungiyar MOPPAN ɗin, lwamanda mai kula da ƙananan hukumomin Fagge Nassarawa da Ungogo da ke cikin ƙwaryar Kano, Sani Musa Bakori ya ce, “A matsayin ‘yan fim na masu wayar da kan al’umma, suna da rawar da za su taka wajen taimaka wa hukumar ta su wajen yaƙi da shaye-shayen da ake yi da kuma fataucin miyagun ƙwayoyi.”
Ya ci gaba da cewa, “A matsayina na wanda ya karanci harkar sadarwa, kuma na san tasirin midiya a cikin al’umma , don haka abu ne mai sauƙi masu shirya fim su isar da duk wani saƙo da ake so nama’a su gani su fahimta. Don haka a wannan zama da za mu yi, zan ɗauki duk wani abu da muka tattauna a rubuce na kai wa magabatana na jiha da na ƙasa, domin su ga irin gudunmawa da ita wannan masana’anta take bayarwa. Kuma ƙofar mu a buɗe take a gare ku ga duk wani da yake so zai shirya fim ko zai yi wani rubutu a kan wani abu da ya shafi harkar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi. Ana iya zuwa a same mu kai tsaye don mu bayar da shawarwari, domin a rinƙa yin su daidai, idan ma ta kama a gayyato mu mu zo wajen da ake gudanar da aikin, don nuna yadda ya kamata a yi aikin duk za mu bada damar hakan.”
Da yake mayar da jawabin sa, shugaban ƙungiyar MOPPAN reshen Jihar Kano, Ado Ahmad Gidan Dabino M O N, ya ce, sun ji daɗin wannan zama na kyautata alaƙar aiki, duk a yake wannan ba shi ne karo na farko da ƙungiyar ta fara zama da hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ba, amma sun ji daɗin wannan zaman.”
Ya ci gaba da cewa, “A baya shugaban hukumar na ƙasa Buba Marwa ya taɓa zuwa an yi zama da ita MOPPAN ta ƙasa, a lokacin Dakta Ahmad Sarari yana shugaban ta na ƙasa.
Amma dai abin da mu masu shirya fim muke fuskanta, sau da yawa idan ka zo ka ce za ka yi fim na tallan wani abu daban, to kai tsaye mutane za su gane su ce talla ne ka ke yi wa wani ko wata ƙungiyar, ko yaɗa wata manufa. To sai ka ga idan ka yi shi don kasuwa, sai ya zama mutane ba su cika damuwa da saƙon ba. Saboda haka, hukumomin da abin ya shafa suna ɗan bada wani tallafi wanda zai zama kai ma ka bayar da taka gudunmawa, su ma su bayar, tun da kai mai sana’a, a matsayin ka na ɗan ƙasa ko ɗan jiha, idan ka ga wani abu da ake yi na karya doka ko lalata tarbiyya, ko ba a baka kuɗi ba za ka yi iya bakin ƙoƙarin ka, don ka ga yadda za ka yi ka hana, matuƙar dai kai ba dilllalin abin ba ne da ba ka so a daina.
Don haka muke kira ga ita wannan hukumar da idan ta ga an yi wani fim da ta ga ya dace tare da yin tallan ayyukan hukumar kai tsaye, ko ya nuna wasu abubuwa, to ya kamata a ɗan samu wani abu a ɗan bayar na nuna wannan fim ɗin an yaba da shi, ga ɗan wani abu. Wannan zai sa mutane su rinƙa ƙoƙarin sassaƙawa, tun da ba za a ce sai an zo an zauna an yi fim gabaɗaya wanda hukumar ce za ta ɗauki nauyi ba. Ta haka ne za a samu kawo hanyar gyaran da ake fata,” inji Ado Ahmad Gidan Dabino.
