Ƙungiyar NAF ta yi martani ga matasan Arewa masu yekuwar a tsige Janar Monguno

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Ƙungiyar Arewa Ina Mafita ta yi kakkausan martani ga wata ƙungiyar matasan arewa mai suna ‘Arewa Youth Assembly bisa kira da suka yi na murabus ɗin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsrao, Janar Babagana Mongonu.

Rahotanni sun ruwaito kakakin ƙungiyar, Mohammed Danlami ne ya yi wannan kira a wata takardar sanarwar manema labarai da ya rattaba wa hannu a ranar Litinin ɗin da ta gabata, inda ƙungiyar tasu ta nemi Janar Monguno da ya yi ritaya ko Shugaba Buhari ya tsige shi.

Sai dai a yayin mayar da martani ga wannan matsaya ta Kungiyar Matasan, Kungiyar Arewa Ina Mafita ta bayyana wannan matsaya a matsayin rashin kishin ƙasa da neman kushe ƙoƙarin gwamnati.

Ƙungiyar Arewa Ina Mafita a wata takardar manema labarai da shugabanta, Mallam Gidado Ibrahim ya rattabawa hannu kuma ya raba ga manema labarai a Abuja, ya ambaci yekuwar da ihun banza.

Ya ce “Cikin alhini muka ga wata sanarwar wasu matasan arewa waɗanda suke kiran kansu da Majalisar Matasan Arewa, inda suke ƙoƙarin kawo hatsaniya a cikin gwamnatin shugaba Buhari ta hanyar yin kira da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Janar Mongonu da ya yi murabus.

“Muna yin amfani da babbar murya wurin bayyana cewa wannan yekuwar ta neman Janar Monguno ya yi ritaya ko a tsige shi maƙarƙashiya ce ta makiya zaman lafiyan Nijeriya, kuma abin takaici ne da ya kamata duk wani kishin ƙasa ya yi tir da shi.

“Wadannan mutanen ba su kallon alherai da irin ayyukan da ofishin NSA din yake yi. Misali, ofis ne bayan samun bayanan sirri ya bayar da shawarar cewa duk wani wuri da ke haɗa cunkoson mutane a kulle shi. Saboda su ‘yan ta’addan suna son yin amfani ne da wuraren da ke da cunkoson mutane masu rauni don su kai musu hari.

“Ba don irin waɗannan kungiyoyi burinsu kawai su haifar da tarzoma da rashin fahimta ba, da sai mu ce, me ya sa suka kauda kai daga irin aikin da ofishin NSA ke yi wurin tattara bayanan sirri, wanda ke taimakawa wurin daƙile hare-haren ‘yan bindiga.” Inji shi.

Daga ƙarshe ƙungiyar ta yi takaicin irin wannan matsaya ta matasan, inda ta ce kamata ya yi su taimaka wa gwamnati da ofishin NSA wurin samarwa da Nijeriya mafita a irin halin da ta tsinci kanta.