Wakilin Sin ya ki amincewa da zargin da Amurka ta yi kan manufofin makamashin nukiliyar Ƙasar Sin

Daga CMG HAUSA

A halin yanzu, ana gudanar da babban taro karo na 10, na dudduba yarjejeniyar haramta yawaitar makaman nukiliya, a hedikwatar Majalisar Ɗinkin Duniya dake birnin New York, inda a kwanan nan, wakilin ƙasar Amurka ya yi zargin cewa, wai ƙasar Sin tana gaggauta haɓaka makaman nukiliyarta, da kin gudanar da shawarwari tare da ɓangaren Amurka, kan batun taƙaita amfani da makaman nukiliya.

Game da irin wannan zargi da Amurka ta yi ba gaira ba dalili, wakilin ƙasar Sin Ding Tongbing, ya bayyana kin amincewa. Ding ya bayyana cewa, ƙasar Sin ba ta yarda da zargin Amurka, kan manufofin Sin game da makamashin nukiliya.

A cewarsa, zargin na Amurka ba zai canja haƙiƙanin gaskiya ba, wato a matsayinta na babbar ƙasa mai yawan mallakar makaman nukiliya, har yanzu, ma’ajiyar makaman nukiliyar ta na ƙara kawo barazana ga zaman lafiyar dukkanin duniya.

Bugu da ƙari, Amurka ta kara ɗaukar wasu matakai, waɗanda suka haifar da babbar illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyya-shiyya da ma duniya baki ɗaya.

Ding ya ƙara da cewa, ƙasar Sin ta dade da ƙoƙarin takaita mallakar makaman nukiliya, don biyan buƙatun tabbatar da zaman lafiya da tsaron kan ta kaɗai.

Jami’in ya ƙara da cewa, kasar Sin ba ta taba shiga takarar makaman nukiliya a lokacin baya ba, kuma ba za ta yi hakan a nan gaba ba. Ya ce maƙasudin ƙasar Sin na mallakar makaman nukiliya shi ne, hana sauran ƙasashe su yi amfani da na su kan ƙasar Sin. Kuma muddin ba su yi amfani da makaman nukiliya kan ƙasar Sin ba, babu buƙatar daukar nata makaman nukiliyar a matsayin barazana, kuma, ba za su ji irin wannan barazana daga ƙasar Sin ba.

Fassarawar Murtala Zhang