Ƙungiyar Tuntuɓa za ta gina cibiyar gyaran hali na masu ta’ammali da ƙwayoyi a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 

Ƙungiyar Tuntuɓa ta bayyana aniyar gina cibiyar gyaran hali na masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a Jihar Katsina.

Shugaban ƙungiyar a Jihar Katsina, Alhaji Aminu Danmusa ya sanar da haka a wata hira da manema labarai a Katsina.

Ya ce, ƙungiyar tuntuɓa na nan na tattaunawa da gwamnatin jihar Katsina domin samar da filin gina cibiyar da babu irin ta a Nijeriya.

Danmusa ya bayyana cewa ƙungiyar ta fara tuntuɓar masu ruwa da tsaki da suka haɗa da gwamnati, masu hali, Sarakuna da malamai domin bada tasu gudunmawa wajen samar da cibiyar.

Ya ƙara da cewa, tunda farko sun sami tsarin yadda cibiyar zata kasance daga wata kamfanin gine-gine a ƙasar Scotland da ita ma take irin wannan cibiya da muke ƙoƙarin sanarwar.

“Bayan kammala ginin, cibiyar za ta kasance wurin gyara tarbiyyar matasa musa ta’ammali da koya masu sana’o’in hannu wanda zai maida su cikin al’umma su zama mutane na gari,” inji Danmusa.

Ya sanar da cewa a wannan shekara kawai ƙungiyar su ta gudanar da tarurruka da masu unguwanni da Magadai da kafafen yaɗa labarai domin suma su bada tasu gudunmawa wajan yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.

Danmusa ya ce rahoton da su ke samu an sami raguwar masu ta’ammali da kwayoyi a jihar, wannan kuwa acewarsa ba zai rasa nasaba da ƙoƙarin da ƙungiyar tayi wajan taron faɗakarwa da kuma ganawa da masu unguwanni da Magadai akan shanye share.

Shugaban ƙungiyar ya bayyana cewa a shekara mai zuwa za su mai da hankali wajan taron gangami kan yaƙi da fatara da yunwa.

“Zamu shirya taron gangami inda zamu gayyaci kwararru masana da zasu gabatar da ƙasida kan illar fatara da talauci ga al’umma da hanyar samun mafita,” inji Aminu Danmusa.

Sai ya yi kira ga masu wadata da su fito su bada ta su gudunmawar wajen taimakawa gwamnati a ƙoƙarin da ta keyi na magance fatara da rashin aikin yi jihar 

Danmusa ya yi bayani kan shirya wannan gangami da ya ce bincike da hukumar ƙididdiga ta ƙasa ta gudanar shekara biyu da suka wuce kashi 74% na al’ummar jihar na zaune cikin fatara da yunwa wanda hakan babban barazana ne ga tsaron jihar.

By ukarofi