Ƙungiyar ’yan jarida a Kebbi ta sha alwashin yaƙi da masu ɓata mata suna

Spread the love

Daga JAMEEL GULMA a Kebbi 

Ƙungiyar ’Yan jarida ta Nijeriya, reshen jihar Kebbi ta sha alwashin saka ƙafar wando ɗaya masu neman ɓata mata suna.

Shugaban ƙungiyar na reshen jihar ne Malam Garba Muhammed Yeldu ne ya yi wannan bayani a wani taron hadingwiwa tsakanin jami’an tsaro da yanjarida da ke aiki a jihar a karshen makon da ya gabata.

Malam Garba Muhammed Yeldu ya bayyana cewa ƙungiyar ta samu rahotanni daban-daban da ke nuna cewa akwai waɗansu da ke kiran kansu ’yan jarida da ke yawon ƙofa-ƙofa suna  addabar jami’an gwamnati, ‘yan siyasa da ’yan kasuwa suna barazanar ɓata sunayensu ko kuma su ba su kuɗi.

Ya ƙara da cewa, ƙungiyar ’yan jarida reshen jihar Kebbi ba za yi zaune ta rungume hannu tana kallon ire-iren waɗannan ɓata-gari suna cin karensu ba ba baka ba wanda ɓata sunan aikin jarida e a jihar ta Kebbi.

Saboda haka ne wannan ƙungiyar ta shirya taron haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da ita saboda a tabbatarwa duniya za a ɗauki duk matakin ladabtarwa da ya kamata sannan kuma a farfaɗo da kimar aikin jarida a jihar.

Mataimakin shugaban ƙungiyar na kasa reshen Arewa ta yamma Alhaji Muhammed Tukur Umar Dutsinmari ya jaddada goyonbayan ɗaukar matakin da ya dace ga duk wanda aka kama da sojan gona a cikin aikin jarida.

Ya kuma yi amfani da wannan damar ya yi kira ga waɗanda abin ya shafa da su riƙa biyan harajin da ke kan kowane ɗan jarida kamar yadda dokar ƙungiyar ’yan jarida da ta ƙasa ta tanada.

Jami’an tsaro da murya ɗaya sun goyi bayan ɗaukar wannan matakin tare yin aiki tare don samun nasarar kawar da irin waɗannan ɓata garin.

Taron da ya sami halartar dukkan ɓangarorin da ya shafa da suka haɗa da ƙungiyar ‘yan jarida (NUJ)  ta jihar Kebbi, wakilan manyan kafafen yaɗa labarai da ke aiki a jihar (Correspondence Chapel) da kuma jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda da jami’an tsaro na farin kaya (Civil Defense) da saurasu.

By ukarofi