Gwamnatin tarayya ta cimma yarjejeniya da ƙasar Haɗaɗɗyar Daular Larabawa (UAE) na baiwa masu fasfo ɗin Nijeriya damar samun bizar tafiya zuwa kasar ta daga yau 15 ga Yuli, 2024.
Ministan yaɗa labaran Nijeriya Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a yau Litinin, lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar Gwamnatin Tarayya bayan kammala taron majalisar zartarwa ta Tarayya.
Sanarwar ta zo ne fiye da shekaru biyu bayan da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta dakatar da bayar da biza ga ‘yan Nijeriya bayan da aka ɗauki tsawon lokaci ana takaddamar diflomasiyya da kasar da Nijeriya.
Hakan kuma na zuwa ne kimanin watanni biyu bayan da kamfanin jiragen sama na kasar “Emirates Airlines” ya sanar da dawo da zirga-zirgar jiragen sama zuwa Nijeriya. Kamfanin jirgin ya ce a watan Mayun da ya gabata zai ci gaba da tashi daga Legas zuwa Dubai daga ranar 1 ga Oktoba, 2024.
Kamfanin jiragen sama na Emirates ya dakatar da zirga-zirgar jiragensa na Dubai-Lagos a shekarar 2022 saboda gazawarsa na maido da kuɗaɗen da suka maƙale a Nijeriya.
