Gwamnatin Tarayya ta tabbatar cewa muna fuskantar matsalar rashin abinci a ƙasar, amma ta bada tabbacin cewa farashi zai daidaita nan ba da jimawa ba.
Aƙalla an samu ƙarin hauhawar farashi da kaso 40% kamar yadda alƙaluma ke nuni daga hukumar ƙididdiga ta ƙasa.
Amma ƙaramin ministan Noma, Aliyu Abdullahi yace gwamnati na ta fitar da tsare tsare wanda nan bada jimawa za su janyo farashi ya fara sauka
Ya bayyana cewa in mun lura yanzu lokacin damina muke. Kuma gonaki cike suke da shuka, don haka sai anyi girbi abubuwa zasu fara dawowa yadda yakamata.
Yace ma’aikatar zata dage wajen ganin an fara ɗaukar noman rani da muhimmanci.
