Yadda darajar Naira ta farfaɗo a kasuwar canji

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Darajar Naira ta farfaɗo bayan ta jera kwanaki tana facuwa a kasuwar ’yan canji.

Naira ta ƙaru da kaso 0.98% zuwa N1,525 a dala 1 a ranar, 5 ga watan Yuli daga N1,535 a dala 1 da aka yi cinikinta a ranar 4 ga watan Yuli.

’Yan kasuwar canji waɗanda aka fi sani da BDC suna siyan kowace Dala a kan farashin N1,500 yayin da suke siyarwa a kan farashin N1,525, inda suka sanya ribar N25.

A kasuwar gwamnati, darajar Naira ta farfaɗo bayan ta kwashe kwanaki uku tana faɗuwa ƙasa warwas.

A cewar bayanai daga kasuwar hada-hadar kuɗi ta FMDƘ, an yi cinikin Naira kan farashin N1,509 a dala 1 a ranar 5 ga watan Yuli, wanda hakan ya nuna an samu ƙarin kaso 0.7 daga farashin da aka sayar da ita na N1,520 a dala 1 a ranar 4 ga watan Yuli.

Daga ranakun 1 zuwa 4 ga watan Yulin 2024, darajar Naira ta faɗi a kasuwar ’yan canji da kasuwar gwamnati kafin ta farfaɗo a ranar 5 ga watan Yulin 2024.

A ranar 2 ga watan Yuli, darajar Naira a kasuwar ’yan canji ta karye zuwa N1,515 a dala 1 daga farashin N1,510 a dala 1 da aka yi cinikinta a ranar 1 ga watan Yuli.

Daga ranakun 3 zuwa 4 ga watan Yuli, darajar Naira ta ƙara faɗuwa zuwa N1,520 da N1,535, bi da bi.

A kasuwar gwamnati, darajar Naira ta faɗi zuwa N1,509, N1,512, da N1,520 daga ranakun 2 zuwa ga watan Yuli bi da bi.

By ukarofi