Daga USMAN KAROFI
Gwamnatin Tarayya ta raba bashin N32.8 biliyan ga ɗalibai 169,000 a ƙarƙashin shirin rancen ilimi na ƙasa (NELFUND). Ministan bayanai, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da aka shirya don nuna nasarorin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Ya ce an raba bashin ne domin taimakawa ɗalibai su biya kuɗin makaranta da kuma tallafin rayuwa.
A cewar ministan, an biya N20 biliyan don kuɗin makaranta, yayin da aka bayar da N12.8 biliyan don tallafin rayuwa ga ɗaliban. Ya ƙara da cewa wannan shiri yana daga cikin manyan alƙawura da Shugaba Tinubu ya ɗauka kafin ya hau mulki, kuma gwamnatin sa tana kokarin tabbatar da cewa kowanne ɗalibi mai buƙata ya samu rance ba tare da wata matsala ba.
Baya ga batun rancen karatu, ministan ya bayyana wasu nasarori da gwamnati ta samu a fannoni daban-daban. Ya ce a shekarar 2024, sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda sama da 8,000 tare da cafke 11,600. Haka kuma, sama da mutane 8,000 da aka sace sun samu ‘yanci, lamarin da ya inganta tsaro a wasu yankunan ƙasar.
A ɓangaren tattalin arziki, ministan ya ce Najeriya ta samu jarin sama da dala biliyan biyar daga kamfanonin mai da iskar gas. Haka kuma, farashin Naira ya ƙaru sosai a kasuwannin hada-hadar kuɗi, yayin da adadin jarin da ‘yan ƙasashen waje ke zubawa a Najeriya ya ƙaru daga kaso 4% a shekarar 2023 zuwa 16% a shekarar 2024.
