Askin taron karatun Alkur’ani ya zo gaban goshi

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Yanzu dai ƙidayar kwanaki a ke yi zuwa ranar da za a gudanar da gagarumin taron karatun Alkur’ani a Abuja. Darajar wanda ya haddace Alkur’anul Karim daban ta ke a nan duniya har gobe kiyama. Don haka ya zama abun albishir ga jama’a don alheri zai sauka a Abuja na gagarumin taron alarammomi daga dukkan yankuna da kabilun Nijeriya. Taron nan irin sa na farko ƙarƙashin inuwar mai alfarma Sarkin Musulmi Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar da manyan malamai daga dukkan ƙungiyoyin Islama zai gudana Insha Allah ranar asabar 23 ga watan Sha’aban 1446 daidai da 22 ga watan nan na Febreru 2025 a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja. Baje fasahar hafizai ta hanyar tilawar Alkur’ani ba gargada, rubuta Alkur’anin da ma fara aikin tarjamar ma’anonin Alkur’ani da rubutun ajami ƙalilan ne daga abun da gagarumin taron ke kunshe da su.

Sanrwar wannan taro na cewa “Alkur’ani littafin Allah. Ka karanta ka samu lada mai yawa ka saurara ka samu lada mai yawa. Mu taru a inuwa ɗaya da alarammomi na Islamiyya da tsangaya” Kazalika an buɗe dandalin yanar gizo ta inda za a yi rajista don wannan taro. Duk wanda ya shigo babban birnin Nijeriya Abuja zai tabbatar da shirin gudanar da wannan gagarumin taro da haƙiƙa a iya sani na shi ne irin sa na farko. Ba za a rasa masu sukar gudanar da taron ba musamman lokacin da a ka ambace shi da babban biki wato FESTIɓAL amma masu shirya taron sun sauya wannan suna don ya zama maslaha ga fahimtar al’umma ya koma gagarumin taro wato CONɓENTION. Ba lallai sai malamai ba hatta sauran jama’a na bayyana ra’ayin su kan wannan taro da nuna fatar ya zama hanyar sada zumunci tsakanin alarammomi da ƙarfafa guiwar mahaddata Alkur’ani su cigaba da karantar da littafin Allah ga masu tasowa. Shi dama karatun Alkur’ani ko haddace rabo ne ga dukkan Musulmi. Za a iya samun musulmi da dama ba su haddace Alkur’ani ba amma su kan iya karanta littafin da sauraron tilawar haziƙai ko gwanayen makaranta. Haƙiƙa akwai lada mai yawa ga mai karantawa da mai sauraron masu karatun Alƙur’ani. Zai zama babban abun farin ciki ga dukkan musulmin da ya yi nazari cewa wannan taron wata nasara ce da za ta ƙara karrama mahaddata da wasun su ma ba su taɓa fitowa daga karkarar da a ka haife su ko garuruwan da su ka zauna tsawon shekaru sun a hidima ga littafin Allah ba. A kan samu wasu masu hannu da shuni da kan gayyaci mahaddata su kwana su na karatun Alkur’ani ko su taru su yi sauka na izu 60 na wannan littafi na Allah. Waɗanda su ka samu fikirar tara dubban makaranta a waje daya su taru su yi karatu su kuma san juna sun yi aikin da sun cancanci addu’ar samun jagora daga wajen Allah. Alamu na nuna in Allah ya sa an kammala wannan taro wasu masu hannu da shuni da ke da shaukin masu karatun Alkur’ani za su riƙa tara mahaddata a matakin ƙaramar hukuma, jiha zuwa shiyya. A gaskiya koyaya mutum zai fassara taron, ba zai kushe mahaddata ba sai dai watakila ba mamaki fuskokin da ya gani cikin malamai da ke shirya taron da ba ya kaunar hada tabarma ɗaya da su. Kuma bincike ya nuna alarammomi musamman na tsangaya a faɗin Nijeriya na farin ciki da wannan taro.

Kamar yanda na ambata a sama alamun shirye-shiryen gudanar da babban taron na  hafizan alkur’ani mai girma sun kankama a Abuja inda manyan allunan sanrawa kan taron su ka bayyana a muhimman sassan birnin.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da a ke cigaba da muhawara kan dalilan taron da ya ke irin sa na farko a Abuja a bayanan tarihi da a ke da su.

An ga matasa da ke goyon bayan taron na gangamin maraba da shirye-shiryen da a ke yi da jan hankalin waɗanda ke sukar hakan da su sauya tunani.

Murtala Garba na daga fitattu a matasan da ke cewa taron zai kara kawo hadin kai a tsakanin makarnta na sassa daban-daban na Naijeriya “mun godewa Sarkin musulmi kuma mun godewa manyan malaman mu waɗanda su ka ba shi goyon baya Sheikh na mu Sheikh Dahiru Usman Bauchi da kuma babban shugaban mu na JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau da kuma Shehum mu Karibullah. Mu na kira ga matasan mu su fito wannan taron don duk inda a ke karanta Alkur’ani akwai albarka a nan.”

Taron dai wanda zai gudana ƙarƙashin Majalisar ƙoli ta Islama ƙarƙashin mai alfarma Sarkin Musulumi Muhammad Sa’ad Abubakar na da zummar tara dubban alarammomi don su yi karatu a ruwayoyin karatu kuma daga dukkan ƙungiyoyin Islama da su ka hadɗa da sufaye, salafawa da sauran su.

Na tambayi shugaban kwamitin fatawa na Majalisar ƙolin Sheikh Shariff Ibrahim Saleh kan muhimmanci ko ingancin taro na kartun alkur’ani “saboda haka karatun Alkur’ani saboda a samu nasara a wurin Allah kan haɗin kai ko sauran su; shari’a ba ta hana ba amma kuma ba ita ce aiki kurum ba, ya kamata duk mutane masu zama wuri ɗaya su hada kan su don su amfani kan su da jama’ar da su ke tare da su. Saboda haka mu na so wannan sunna ta rayu har abada”

Duk da a na sa ran shugaba Tinubu zai halarci taron ranar 22 ga watan nan na Fabrairu amma kai tsaye ba wani bayani daga wani jami’in gwamnati da ya alaƙanta abun da siyasa ko bukatar neman goyon bayan jama’a ga zaɓe mai zuwa a 2027 da ke da nisa daga yanzu; da hakan ya saba da zarge-zarge a yanar gizo.

Dattijon ‘yan siyasar arewa Injiniya ƙailani Muhammad ya ce taron zai karfafa karatun tsangaya da gwamnati ta fara maida hankali a kai zamanin tsohon shugaba Jonathan ”a lokacin shugaba Jonathan ya kawo maganar tsangaya da za a taimaka mu su sai mu ka samu akasi a lokacin Buhari a ka soke tafiyar tsangaya. Yanzu lokaci ya yi da za a dawo da shi a kai mu su makarantar boko”

Kwamitin shirya taron da ya hada da manyan malaman Islama ya buɗe dandalin yanar gizo don samar da bayanai ga masu niyyar halartar taron. Bayanai na nuna an gayyaci babban limamin haramin Makkah Sheikh Abdulrahman Sudai don shaida taron.

Ko shara a ka saka ni na filin taron alarammoni a Abuja zai karɓa – Aliyu Kaduna;

Sheikh Aliyu Ibrahim Kaduna da ke cikin malaman da su ka shahara a yanar gizo ya bayyana matsayar sa kan babban taron alarammomi da za a gudanar a Abuja.

Malamin na magana ne a shirin gidan talabijin na KAFTAN Abuja da ya tattauna kan shirin babban taron.

Malamin ya ce ba ma kawai a ce an gayyace shi don gudanar da wani aiki a taron ba, ko sharer filin taron ya samu zai karɓa hannu biyu.

Duk da malamin ya ce bay a cikin masu shirya taron amma a matsayuin sa na sakataren majalisar malamai na Izala a Abuja ya zama kai tsaye mai matsayin gaiyatar jama’a zuwa taron.

Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya nuna muhimmancin irin wannan taro na karatun Alkur’ani mai girma ya na mai cewa in ya ga kuskure na wani abu game da taron ya san inda zai kai bayani don a gyara amma ba ta kafar labaru ba.

Aliyu Kaduna ya ce dama ya na shauƙin lamura da su ka shafi malamai ma’abota tsangaya kuma ga dama ta samu ta karrama ajin waɗannan malaman.

Cikin abun da Allah ya addara an samu matuƙar juyayin labarin gobara da ta shafi wata tsangaya a jihar Zamfara inda almajirai 17 su ka rasa ran su. Haƙiƙa waɗannan almajiran da sauran marigaya da su ka rasu cikin wannan hidima ta karatu za su samu karin addu’o’in rahama a wajen wannan babban taron.

Rahotanni sun baiyana cewa akasin ya afku ne a tsangayar Malam Ghali da ke yankin ƙaramar hukumar Kauran Namoda kuma wutar ta ci tsawon dare inda haka kazalika ya kawo kuna ga wasu almajiran 16.

An ruwaito shugaban kƙƙramar hukumar Kauran Namoda Mannir Mu’azu Haidara na tabbatar da afkuwar ibtila’in.

ƙarin bayanai sun nuna an kai ɗauki inda a ka yi tsammanin an fidda dukkan almajiran da su ka kai 100 daga gidan tsangayar amma bayan wutar ta mutu a ka rika tsintar sawaye da hannayen yaran sun kone ta yanayi mai ban tausayi.

An alaƙanta ruruwar wutar da buhunan hatsi da ke cikin gidan. Tuni a ka yi jana’izar almajiran da su ka riga mu gidan gaskiya.

Kammalawa;

Matuƙar mutum ba zai faɗi alheri ba kan wannan taro ko ba da shawara mai ma’ana to ya fi dacewa ya yi shiru. Haƙiƙa cewa sai lallai mutum ya yi magana da kalmomi masu kaushi don huce haushi ko tunanin samar da gyara da lafuza marar sa kan gado ba alheri ba ne kuma a ƙarshe hakan ba zai haifar da wata riba ba. Aƙalla dai ko mutum ba zai yi fatar a gudanar da wannan taro lami lafiya ba, to ya kaucewa aibanta ma’abota taron da miyagun kalamai da ba zai so a faɗa ma sa ba kuma ko da ya na kan kuskure.

By ukarofi