Daga AISHA ASAS
Mai karatu barkanmu da sake kasancewar a wannan shafi mai muhimmanci na jaridar Manhaja.
A wannan satin na san mai karatu zai ce darasin namu ya ɗan sha kwana, saidai kamar yadda masu karin magana suka ce wai, ‘barin kashi a ciki ba ya maganin yunwa’, bature kuwa na cewa, ‘matsalar da aka tattauna, matsala ce da aka ci kaso hamsin bisa ɗari na magance ta’
Da yawa matsalolin mata da suke gum da bakinsu da sunan kunya na kai su ga babbar matsala da ka iya illata aurensu ko ma lafiyarsu bakiɗaya.
Matsalar jin zafi a lokacin saduwa na taka muhimmiyar rawa a gurɓacewar aure a ƙasar Hausa, domin ta kan haifar da rikici tsakanin ma’aurata, musamman ma kasancewar ba mu cika tattauna ire-iren waɗannan matsaloli ba a tsakanin ma’aurata a ƙasar Hausa
Da wannan ne shi mijin zai ga matar tasa na gudunshi ne, ita kuma ba za ta iya yi masa bayanin abinda take ji ba.
A sati biyu da suka gabata, ina wata asibiti a wata uguwa a cikin Jihar Sakkwato, an kawo marar lafiya mace da goyonta, wadda yarinyar ba za ta wuce watanni huɗu ba, uwar wadda ta kasance ba ta jin Hausa sosai, don haka likitan ya juya ga mijita wanda ya kawota, yana masa tambayoyin da yake son sani kafin ya ba ta kulawar da ya dace.
Tambayoyin kuwa su ne; mararta na ciwo? Yaushe ta gama al’ada? Tana jin zafi yayin saduwa?
Dukka waɗannan tambayoyi ne da ya kamata ace miji ya san da su, saidai wannan bawan Allah da matar ta shi ke kwance tana jijigga tamkar ƙwallon da aka buga, ya kasa amsa su, ya juya baki ya yi mata magana, a tunaninmu ya tambaye ta ne, don haka da ya sanar da likitan cewa, marata ba ta ciwo, da rashin jin zafi, da sauran tambayoyin dukka sai muka amince.
Saidal da marar lafiyar ta fara farfaɗowa, likitan ya yi mata magana irin ta kurame, don a cewarsa, ya lura mijin kunyar matar yake yi (har muna ta yi wa likitan dariya), a nan ya tabbatar da bai tambaye ta, domin ta amsa da kishiyoyin abinda mijin ya faɗa, wanda zargin likitan ya zama gaskiya
Da irin wannan ne matsalar zafi yayin saduwa ke dasa ƙiyayya da rikici a gidaje da dama. Duk da a wasu lokuta magani kaɗan ki ke buƙata don kawar da ita.
A baya, matsalar zafi yayin saduwa ya mamaye kaso ashirin ne bisa ɗari na mata, saidai daga baya ya zama wutar daji, inda adadin mata da ke ɗauke da shi suka linka adadin.
Kada ki ji na faɗi yuwar magance shi cikin ɗan ƙanƙanen lokaci ki ɗauka ba komai ba ne, domin dalilai mabambanta ne ke haddasa hakan ga mata, wanda ba lalai, irin dalilinka ya zama ɗaya da na ƙawarki ba.
Abin nufi a nan, yakan yiwu a same shi a dalilin wasu ɗabi’u da ki ke yi wa farjinki wanda ba ya son hakan, wanda zai haifar da wani abu da zai haddasa ma ki matsalar, kuma zai iya yiwa ya zama wata alama ta wata cuta, wadda ta zafin ne take ƙoƙarin fahimtar da ke zuwanta, kinga kuwa a cikin kowanne yanayi, zuwa asibitin dai shi ya fi, don gujewa cuta daban magani daba
Duk da cewa, lokuta da dama matan suna bayyana halin da suke ciki don neman mafita, ko dai ga masu maganin mata, ko na gargajiya, ko kuma a tsakanin ƙawayensu, saidai hakan bai cika tasiri ba, domin suna kai kuka ne a inda ba a iya magance masu matsalar. Domin masu kayan matan za su yi ƙoƙarin ba su ababen da za su ƙara masu sha’awa ko ni’ima ba tare da la’akari da yiwar wani dalilin daban ba.
Wasu kuwa suna sanar da su cewa ba matsala ba ce, su mayar da shi wani abu na halitta, wato mata na jin zafi yayin saduwa, don haka ba shi da magani saidai haƙuri.
Kada in ja ku da dogon zance, yana da kyau ki san ababen da ka iya janyo ma ki zafi yayin kwanciyar aure, saidai fa ba yana nufin ki canka daga ciki ba, ma’ana ki zaɓi wanda ya fi maki ki ce shi ne matsalar ki ba. Kamar yadda na faɗa, zuwa asibiti a tabbatar ne mafita
Bushewar farji: Wata hanya ce mai sauƙi da za ta iya kawo zafin saduwa, idan na ce mai sauƙi, ina nufin ƙarama da za a iya kawo ƙarshenta cikin sauƙi. Saidai abu na farko da za ki tambaye kanki shin me ya kawo ma ki bushewar gaba?
Za mu ci gaba a mako mai zuwa.
