Ɗan uwana ne ya miƙa ni ga masu garkuwa, inji wata mata a Kotu

Babbar kotun jihar Kaduna da ke zama a unguwar Dogarawa ta garin Zariya, ta ɗage ci gaba da sauraron ƙarar da ake yi wa Abubakar Halliru bisa zargin hannunsa a garkuwa da wata ’yar uwarsa zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu 2022.

Ana dai tuhumar Abubakar Halliru kan zargin kai wata ’yar uwarsa wajen masu garkuwa da mutane domin karvar kuɗin fansa.

A yayin da take bayar da shaidar abin da ya faru a tsakaninta da Abubakar Halliru, Hajiya Binta Muhammad ta yi wa kotu bayanin cewa, shi wanda ake tuhumar ɗan uwanta ne kuma ta amince da shi matuƙa don haka a ko yaushe ta ke kyautata masa zato.

A cewarta, la’akari da yadda ta amince da shi shi ya sanya suke harkar kasuwanci inda har ta danƙa masa kuɗinta naira miliyan 3 da dubu 98 a hannunsa domin a juya mata.

Sai dai ta ce, duk tsawon lokacin da suka shafe suna harkar kasuwancin, ba ta taɓa neman ya bata wani abu ba sai a ranar 8 ga watan Agusta 2021 da ta buƙaci da ya ba ta wani kaso daga cikin kuɗin amma ya yi burus da ita.

Ta ce, ya daina ɗaukar wayarta idan ta kira shi, sai a ranar 10 ga watan Agustan bara ne ya kirata yana tambayar inda zai same ta.

“Sai na sanar da shi cewa ina kasuwar Sabon Gari, amma sai ya buƙaci da in same shi da zummar cewa za mu haɗu da wani Alhaji Salisu unguwar Ɗan Magaji wanda a wurinsa zai karvi kuɗina ya ba ni. Sai na turje da cewa harka ce tsakaninmu ba sai wani ya shiga ciki ba, don haka na ce ba wurin wanda zan je. Amma sai ya kafe a kan lallai sai mun je wurin Alhaji Salisu da ya ce, sai in ya ganta ne sannan zai bayar da kuɗin, wanda daga haka ne sai na yarda na bi shi muka tafi,” inji ta.

Ta ƙara da cewa, “bayan na kira shi don na tuntuɓi wurin da za mu haɗu, sai ya ce na same shi a shataletalen Kano yana jirana a nan. Sai na ɗauki mota ta na je har wurin na same shi, na kuma miƙa masa mukullin motar don ya tuƙa, kuma daga nan muka kama hanya. Ko da na ga mun kai Danmagaji bai tsaya ba zai wuce, sai na tambaye shi ya za ka wuce sai ya ce ai Alhaji Salisun ya turo masa da saƙon tes cewar ya tafi gida sai dai mu same shi a can.

“Mun kai hanyar da ta nufi Galadimawa sai ya kira waya na ji yana cewa gamu nan zuwa nan da minti 20 za mu iso. Sai na ce da shi ai tafiyar minti 20 akwai nisa kuma ga shi an ce hanyar ba ta da kyau, amma ya yi shiru bai ce min uffan ba. Muna cikin tafiya sai ya saki babbar hanyar ya bi wata ƙaramar hanyar inda muka haɗu da wasu mutane biyu suna tsaye a gefe da gefen hanya rataye da bindiga ƙirar Ak47 a kafaɗunsu.”

“Sai na razana na nemi ya koma da baya ina ta addu’a, amma ya ƙi sai da ya kai inda suke ya tsaya kuma suka umurcemu da mu fito.

“Da muka fito daga motar sai suka ce mu zauna daga nan sai wani daga cikinsu ya mare ni suka tasa mu zuwa wajen sauran abokansu da ke gaba inda wani ya karyo itace ya riƙa dukana.

“Daga nan sai jagoransu ya umurci ɗaya cikinsu da ya ɗaukeni a kan babur ya tafi da ni tsauni, na riqa roqon da su haɗa ni da ɗan uwana a wuri ɗaya, kuma don Allah kar su yi masa komai nan ma suka ci gaba da dukana sai na hau aka tafi da ni.

“Bayan wani ɗan lokaci sai ga sauran har da shi ɗan uwan nawa suka same mu a tsaunin inda suka ce naira miliyan 100 suke so a hannuna, sai na ce musu ba ni da wannan kuɗin amma su kyale ni kar su tava lafiya ta zan ba su iya abinda nake da shi.

Hajiya Binta ta ci gaba da bayyana wa kotun cewa, bayan dare ya soma yi ne sai suka tafi suka bar mutum ɗaya don ya yi gadinta har zuwa safe tare da sanar da ita cewa ta yi tunani kan kuɗin don idan babu za su kasheta.

Ta ce, Allah cikin ikonsa, sai barci ya fara kama wanda ke tsare da ita sai ta ɗauki dutse ta yi jifa sai ya tashi firgigi ya kewaya don ganin ko mene ne, bayan da ya dawo sai ya ce mani da akwai alamun haɗari za a yi ruwan sama daga nan sai ya shiga cikin bukkar da tabarmarsa ya kwanta kusa da ni a nan kuma sai barci ya ɗauke shi.

“Ni kuma da naga haka, sai na lallaɓa na tsere duk da ana ruwa, amma saboda rashin sanin inda zan nufa sai na faɗa hannun wasu masu garkuwa da mutane inda suka ce za su taimakeni, koda yake an basu cigiyar wata wadda ta tsere, sai na ce bani ba ce sai suka tafi da ni sansaninsu, a can ne suka ce su na buƙatar naira miliyan 30.

“Bayan na kwashe mako takwas a hannunsu, daga nan sai suka ce in ba su lambar da za su yi magana don a kawo musu kuɗin sai na ba su lambar kuma aka daidaita da su a kan naira Miliyan 5 da dubu 500 da wayar hannu guda 2 da katin waya na naira dubu 70.

“Da aka cika musu buƙatunsu ne suka sake ni inda da na ya ɗauko ni ya wuce da ni asibiti Salama da ke Kwangila inda na kwana huɗu ana duba lafiyata saboda sun ce akwai zazzaɓi mai ƙarfi tare da ni kuma jinina ya yi ƙasa.

“Bayan an sallame ni daga asibiti sai muka tafi ofishin ’yan sanda da ke Danmagaji inda na shigar da koken abinda ya faru da ni, a cewarta.