Rasha za ta ci gaba da tsayawa kan bakarta kan lamarin Ukraine

Sakataren harakokin wajen Amurka Antoni Blinken, ya buƙaci Rasha da ta gaggauta bada haɗin kai don sauƙaƙa wutar rikicin da ke ƙara ruruwa tsakanin ta da Ukraine a yunƙurin da ta ke yi na mamaye ta.

Blinken wanda ke waɗannan kalamai a yayin tattaunawar sa da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov, inda ya ce hanyar da Rasha za ta bi wajen sauƙaƙa wannan al’amari kuwa shi ne, janye dakarun da ta jibge kan Iyakar Ukraine.

Blinken ya kuma jadadda cewa, duk wani yunƙuri na ci gaba da mamaye Ukraine daga Rasha, zai janyowa ƙasar tashin hankali ta ɓangarori mabanbanta, inda ya ce, hanyar diplomasiya ce kaɗai ya kamata Rasha ta bi wajen warware al’amarin.

Sai dai a nasa ɓangaren Lavrov, ya ce, yayin tattaunawar sa da Blinken, ya jadadda cewa, Rasha za ta ci gaba da tsayawa kan buƙatunta, musamman waɗanda suka shafi kare tsaron ta.

Wannan tattaunawar dai na zuwa ne bayan da ake ci gaba da musayar yawu tsakanin ƙasashen yamma da Rasha, dai-dai lokacin da ake zargin ta da afkawa Ukraine ta ƙarfin tsiya.