2023: APC ta musanta raba muƙamai ga shiyya-shiyya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya ta nesanta kanta daga wani jerin sunaye da ya ke ta zagaye a kafofin sadarwar zamani, inda takardar ke nuni da yadda jam’iyyar ta raba muƙamai shiyya-shiyya, kuma a ka ce Shugaban Riƙon Ƙwarya na jam’iyyar, Mai Mala Buni ne ya sanar da shi.

Hakan ya fito ne a wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na jam’iyyar APC, Mamman Mohammed ya sanya wa hannu a ranar Laraba.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “an janyo hankalin Gwamnan Jihar Yobe kuma Shugaban Kwamitin Rikon Ƙwarya na Jam’iyyar APC, Mai Mala Buni ga kafafen yaɗa labarai tare da zargin cewa shi ne ya sanar da raba ofisoshin a shiyya-shiyya.

“Ya musanta jerin sunayen da ake ta yaɗawa, yana mai cewa, ƙarya ne, marar tushe, yaudara ce kuma ba shi da alaƙa da shi.”

Buni ya ce jam’iyyar APC ba ta ɗauki wani mataki a kowane fanni kan wani abu da ya shafi shiyyar ofisoshin ba.

Ya ce, “kawai ina tunanin marubucin ne da ba shi da alaƙa da shugaban jam’iyyar da ma jam’iyyar baki ɗaya.

“Ana kira ga jama’a da su yi watsi da jerin sunayen da ake zargin cewa yaudara ce kuma gaba ɗaya ƙarya ce.”

Shugaban ya buƙaci ‘yan jarida da su bijire wa labaran da ba a tabbatar da su ba, da kuma jita-jita, da tabbatar da duk wani abu da ya shafi jam’iyyar, tare da yin alƙawarin cewa ƙofofin jam’iyyar a buɗe suke don neman bayanai.