Saki boka, ki kama Allah (1)

Daga SALIHA ABUBAKAR ABDULLAHI ZARIYA

A cikin ɗabi’un ɗan Adam a kan samu waɗanda son kansu fiye da waninsu kan yi tasiri cikin rayuwarsa, duk da ba dukka zukata ne ba sa juyawa ga bigiren aikata alkhairi ba, duk da haka akan yi la’akari da aiki a aikace ga duk jinsin da suka faɗo cikin filin wannan aikatau ɗin.

Asiri, magani, sammu ko makaru dukkansu kalma ɗaya ce da ke nuni da abu guda. Ko ka yi ko kuma a yi maka. Duk da akan ce mai baya bai yankar ƙauna, domin ko ba ka haifa ba an haifar ma ka, sai dai yawancin mutane wannan tunanin bai zuwa mu su musamman mata waɗanda idonsu kan rufe, shaiɗan ya samu damar busa mu su sarewarsa suna taka rawa.

So da yawa akan ci karo da matan da ke kauce hanya tare da yin biris ko nuna halin ko-in-kula da dokokin addininsu na Islama, su shiga su fita gidajen bokaye da malaman tsibbu su tsundumma neman wasu buƙatocinsu ta haramtacciyar hanya don mallake mazajensu, korar kishiya, hana miji ƙara aure, hana kishiya zama lafiya da mijin, ko saka mata wata cuta, yayin da wasu kan maida hankali wajen dasa ƙiyayya tsakanin ɗa da mahaifi, ko a lalata hanyar sana’ar wata, ko a hana wa rayuwar wata saƙat ta hanyoyin surkulle kala-kala don kawai son kai da rashin sanin ya kamata, ko a ce sakaci da riƙon addini wanda hakan bai wanzuwa face an samu ƙarancin imani cikin zukata.

Da yawa mata kan samu raunin tunanin da ke kai su jefa kansu cikin hallaka da shiga cikin halin ha’ula’i, ya Allah a dalilin son zuciya ko zugar ƙawaye ko kuma gurɓatacciyar tarbiyyar da ta samo usuli tun daga wajen iyaye mata a inda so tari hakan kan janyo mu su inda-na-sani lokacin da suka farga ko suka ankaro, ko da yake waɗanda suka shiga cikin irin wannan mummunar ɗabi’a ba kasafai su kan tuna cewa Allah ne ke ikon komi da kowa ba, wasu lokutan har lokaci ya ƙure mu su sosai kafin su dawo su yi nadama maras amfani.

Haƙiƙa irin waɗannan mata cikin kowanne lokaci su kan manta da Mahaliccinsu ne mai biyan buƙatan bayinsa cikin kowanne yanayi komin wuya komin daɗi, sai su ɗauki ta su buƙatocin zuwa ga wanin Mahaliccinsu ba tare da la’akari da cewar shi kanshi bokan bai san abinda zai faru da shi yanzun ko anjima ba, amma zuciyarsu ta ƙeƙashe a ƙoƙarin samun mafitar da gurbataccen tunaninsu ya nuna mu su itace hanya mai ɓullewa a garesu.

Ba tunanin ɗimbin zunubin da ke tattare da wannan aikin, ba tunanin cewan suna aikata laifi ne ma fi muni a wurin Allah SWT, domin shirka ce ƙarara suke yi, ba tsoron Allah, ba tunanin makomarsu gobe ƙiyama.