Jakadan Bauchi: Kwance rawanina zancen baki ne kawai, inji Dogara

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi

Tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Rt. Hon. Yakubu Dogara ya danganta dakatar da sarautar sa ta gargajiya na Jakadan Bauchi da majalisar masarautar Bauchi ta yi a ranar Litinin da ta gabata a matsayin zance ne na baki wanda bai kai ga zuciya ba.

Ya ce, “kawo wannan rana ta Talata, ba wata takardar dakatarwa da aka bani, kuma har ila yau babu wanda ya sanar da ni cewar, akwai wani ƙagen laifi da ake tuhuma ta da shi a gaban majalisar masarautar Bauchi.”

Da yake numfasawa kan zargin dakatar da sarautar sa ta Jakadan Bauchi da masarautar ta yi a ranar Talata da ta gabata, Dogara ya ce ya yanke shawarar tofa albarkacin bakin sa ne kan lamarin, biyo bayan shawarwarin masu yi masa fatan alheri, har ma da manema labarai kan buƙatar yin hakan, kuma domin gujewa yadda jama’a za su yi hukunci.

Ya kuma danganta dakatar da sarautar sa da aka yi ga wautar rashin sanin illar sakamakon  koken shari’a da gwamna Bauchi ya gurfanar da shi tare da wasu jama’a a gaban kotu.

Dogara ya shaidar cewa, takardar dakatar da sarautar tasa an yaɗa ta ne a yanar intanet bisa takardar bogi ba mai tambari irin ta majalisar masarautar Bauchi ba, wanda ke nuna ayar tambaya, kuma ma dakatarwar ɗumgurungum ɗinta shaci-faɗi ce kurum.

Tsohon kakakin majalisar ya yi jimami da cewar, tsohuwar masarauta irin ta Bauchi ba za ta yi hukunci ko yanke shawara a kan zance maras tushe ba, domin da maganar gaskiya ce, bai wuce mizanin a kira shi domin kare kan sa ba bisa zargin.

Don haka sai ya bayyana dakatarwar tasa a matsayin maƙure masa ‘yancin jin ta bakin sa, yana mai cewar, zargin da aka yi masa na rashin jajanta wa sarakunan Bauchi da Dass dangane da farmaki da aka yi masu, ya ce wannan ma soki burutsu ne.

Dogara, sai ya wallafo saƙon kada ta kwana da ya aike wa sarakunan biyu dangane da farmakin, inda yake cewa, “Allah ya taimaki Mai Martaba, ‘Ina mai da’awar rubuta da miƙa jaje na gare ku bisa abun takaici da ya faru bisa kan hanyar ku daga Bauchi zuwa Bogora a safiyar wannan rana. Wannan lamari ya ruɗar da jama’ar mazaɓa ta, har ma da ɗaukacin jiha baki ɗaya, kuma mun yi tir da faruwar hakan.

“Na so na yi tattaki da kai na domin jajanta wa a madadin jama’ar mazaɓa ta, duk da fahimtar irin wannan ziyara akan yi mata gurguwar fassara kamar yadda ya faru a baya wasu lokuta da ake rufe mun ƙofofin shiga wasu fadoji duk lokacin da na ziyarta yayin da nake riƙe da kujerar kakakin majalisa.”

Dogara, ya bayyana cewar, saƙon jajantawar ya aike wa duka sarakunan biyu, na Bauchi da na Dass, kuma yana da tabbacin wasu shaidu na saƙonnin sun isa ga masu su.

Kamar yadda ya ce, vata lokaci ne ma a ce ba za a iya kaucewa aukuwar wancan mummunan lamari ba, domin gabanin taron ya shaida wa hukumomin tsaro su samu tabbaci daga wajen masu shirya shi kan cewar za a wanye lafiya.

“Saboda haka abu ne na ɓatan basira bisa la’akari da lamarin a ce babu wani abun ƙi da zai faru a wajen taron, musamman ganin yadda aka fara tada jijiyoyin wuya a gabanin taron.

Dogara ya kuma lura da cewar, nuna nadamar faruwar lamarin ma wata alama ce ta yarda da aikata laifi, yana mai faɗin, “ba daidai ba ne majalisar masarautar Bauchi ta hukunta shi bisa zantuttukan kunij-kunji, ko yi masa yarfe.”

Ya ƙara da cewar, “Ina da yaƙini gaba ga Mahalicci na ba ni da hannu a cikin wata taɓargaza ta ƙasar Zaar, har ma wacce ta faru a kwanakin baya da ta shafi sarakunan mu biyu, kuma ba ni da wata masaniya na cewar za su halarci wancan taro da ya nuna alamar gurɓacewa tun kafin a fara shi.
“Don haka, ba ni da ƙarfin gwiwa na cewa an gayyaci sarakunan zuwa wajen wancan taro, kuma ko an gayyace su, babu alamar za su halarta domin ba su saba amsa gayyatar irin wannan taro na ƙasar Zaar ba. Don haka yaya za a ambace ni da hannu a cikin wancan farmaki da ya shafi sarakunan biyu?

Dogara ya ce, ya kuma fahimci cewar tuntuni, Sarkin Bauchi da ‘yan majalisar sa duka suna cikin wani matsi daga gwamnatin jiha na buƙatar janye tawa sarauta ta Jakadan Bauchi.

Ya kuma yi tuni da cewar, Gwamna Bala can a baya bisa take doka ya soke takardun sa guda biyu na mallakar filaye, kamar yadda ya soke na abokin zumuncin sa, Hon Yakubu Shehu Abdullahi, da na wani tsohon gwamna kuma ubangidan sa, ya kuma ci gajiyar sa.