Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta gargaɗi jam’iyyun siyasar Nijeriya cewa, ranar Juma’a 3 ga watan Yuni 2022 ya rage wa’adin gudanar da zaɓen fidda gwanin zaɓukan 2023.
Hukumar zaɓen ƙasar ta fitar da wannan sanarwa ne a ranar Alhamis ta hannun shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a, Festus Okoye.
A cewar Festus Okoye, dukkanin jam’iyyun siyasa na da wata guda daga yau su kammala zaɓen fidda gwani.
Ya jaddada cewa, ya kamata a gabatar da sunayen ’yan takarar shugaban ƙasa da na ’yan majalisun tarayya tsakanin ranakun 10 zuwa 17 ga watan Yuni yayin da na gwamnoni da na majalisun jihohi ya kasance tsakanin 1 zuwa 15 ga watan Yuli.
Sanarwar ta ce, “idan za a iya tunawa, a ranar 26 ga watan Fabrairun 2022, Hukumar ta fitar da Jadawalin Ayyuka na Babban Zaɓen 2023. Ya tanadi jam’iyyu su gudanar da zaɓen fidda gwani na ’yan takara daga ranar 4 ga Afrilu zuwa 3 ga Yuni 2022.
“A bisa bin sashe na 82 (1) na dokar zaɓe ta 2022, dukkanin jam’iyyun siyasa 18 sun ba da sanarwar da ake buƙata da ke nuna ranakun gudanar da babban taronsu da na majalisun tarayya da na ’yan majalisun tarayya da nufin tantance ’yan takara a muƙamai daban-daban na zaɓe kamar yadda kundin tsarin mulki ya kayyaɗe, da kuma dokar zaɓe. Tuni dai wasu daga cikin jam’iyyu suka fara aikin da Hukumar ta tura ma’aikata domin sanya ido kan aikin kamar yadda doka ta tanada.
“Ana ƙara tunatar da jam’iyyun siyasa cewa, dole ne su miƙa wa Hukumar jerin sunayen ’yan takarar da za su fito daga fitattun ’yan takara,” inji shi.
Hukumar ta ce, za ta cigaba da haɗa kai da jam’iyyun siyasa domin tabbatar da bin ƙa’idojin da aka gindaya na dukkan ayyukan zaɓen 2023.
