2023: Bashir Machina ya sake kayar da Sanata Lawan a kotu

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu

A ranar Litinin Kotun Ɗaukaka Ƙara dake zamanta a Abuja ta amince da takarar sanata mai wakiltar Yobe ta Arewa a ƙarƙashin Jam’iyyar APC, Hon. Bashir Sheriff Machina.

Kotun ta tabbatar da hukuncin da Babbar Kotun Tarayyar da ke Damaturu ta yanke tun da farko inda ta bayyana Bashir Machina a matsayin halastaccen ɗan takarar sanatan APC a Yobe ta Arewa.

Bugu da ƙari, Kotun ta yi watsi da ƙarar da Jam’iyyar APC ta shigar kan rashin amincewar da ta sanya ɗaukaka ƙarar.

Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem wadda ta yanke hukuncin, ta ce Babbar Kotun ta Tarayya da ke Damaturu ta yi gaskiya bisa tabbatar da zaɓen fidda gwani na Majalisar Dattawa wanda Jam’iyyar APC ta gudanar ranar 28 ga watan Mayu da ya gabata, wanda ya bai wa Hon. Machina nasara tare da bai wa hukumar INEC ta sanya masa ido wajen aiwatar da shi.

Idan dai za a iya tunawa, jam’iyyar APC mai mulki ta garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara tare da neman a yi watsi da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Damaturu ta yanke, kana ta buƙaci a bayyana Sanata Ahmad Lawan a matsayin ɗan takarar sanata na jam’iyyar a Yobe ta Arewa.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya nemi ya koma kujerarsa ta sanata ne bayan da ya gaza kai bantensa a takarar Shugaban Ƙasa.