Ƙaddamar da ayyukan haƙar man fetur a iyakar Bauchi da Gombe

Assalam alaikum. Da farko dai muna maraba da wannan sabon aiki da za a ƙaddamar a Arewa, wanda a ranar Talata ne ake sa ran shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, zai ƙaddamar da ayyukan bunƙasa haƙar man fetur a yankin Kolmani da ke iyakar jihohin Bauchi da Gombe.

Kamfanin samar da man fetur na Nijeriyar, NNPCL, ya ce shekara biyu da suka wuce ne aka tabbatar da gano tarin arzikin man fetur mai yawan da za a iya sayarwa a yankin.

Wannan ne karon farko da ake haƙo man fetur a Arewacin Nijeriya.

Bayanai sun nuna cewa akwai ƙarin wasu rijiyoyin da aka kammala aikinsu kamar wannan a yankin na Bauchi da Gombe, waɗanda za a ci gaba da aikin samar musu da wuraren da za a sarrafa man fetur da dangoginsa, irin sa na farko a arewacin Nijeriya, kana akwai wasu da dama da ake aikin haƙo man.

Bugu-da-ƙari kuma, bayan Shugaba Buhari ya ƙaddamar da aikin bunƙasa ayyukan haƙar man fetur ɗin, za a ci gaba da aikin haƙo sauran wuraren da aka gano don tantance yawan man fetur da iskar gas ɗin da ke ƙarƙashin ƙasa wanda a za a iya fitar wa tare da sarrafa ɗanyen man fetur ɗin da iskar gas.

Ana sa ran za a gina matatar mai da sauran ayyukan albarkatun man.

Tuni dai al’ummar jihohin Bauchi da Gomben, musamman mazauna yankunan da ake aikin haƙo man fetur ɗin suka bayyana farin cikin su da wannan aiki.

Wasu daga cikinsu sun shaida cewa, sun ji daɗi da aka kawo wannan aiki yankinsu tare da fatan samun alkhairi mai yawa dama samun ayyukanyi ga mazauna wajen.

Sun ce suna fatan kuma aikin bunƙasa haƙar man fetur ɗin zai kawo wa yankinsu ci gaba da zaman lafiya mai ɗorewa.

A shekarar 2016 ne kamfanin mai na Nijeriya NNPC, ya ƙaddamar da aikin binciko man fetur a arewacin ƙasar, abin da ya kai ga gano ɗimbim albarkatun man fetur ɗin a jihohin Bauchi da Gombe da Borno da kuma jihar Neja.

Nijeriya dai ita ce ƙasar da tafi kowacce fitar da ɗanyen mai a kasuwannin duniya a nahiyar Afrika, sai dai kuma takan kashe maƙudan kuɗaɗen wajen shigo da tataccen man da ake amfani da shi a cikin ƙasar saboda lalacewar matatun man ƙasar.

A lokuta da dama gwamnatoci daban-daban sun sha lasar takobin gyara matatun man ƙasar domin wadatar da ita da man take buƙata, amma daga baya sai maganar ta bi shanun sarki.

Amma a yanzu rahotanni an ambato gwamnati na cewa gano ɗimbin man da aka gano a arewacin qasar zai ƙara yawan man da ƙasar ke haƙowa a kullum tare da samar da wurin da za a riƙa tace shi.

MUSTAPHA MUSA, 08168716583.