Daga CMG HAUSA
A baya bayan nan, hukumar sadarwa ta Amurka, ta fitar da sanarwa dake cewa, an haramtawa kamfanonin ƙasar Sin da dama sayar da kayayyakin da ake amfani da su a harkokin sadarwa da na sanya ido a Amurka.
Da yake tsokaci game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yayin taron manema labarai na yau Litinin cewa, matakin Amurka ci gaba ne da fakewa da batun tsaron ƙasa wajen keta hakkokin kamfanonin Sin, tare da amfani da ƙarfin iko ba bisa ƙa’ida ba.
Zhao ya ce Sin na matuƙar adawa da waɗannan matakai, wadanda suka keta ƙa’idojin cuɗanyar tattalin arziki, da karya dokokin cinikayyar ƙasa da ƙasa, da gurgunta moriyar kamfanonin ƙasar Sin.
Mai fassara: Saminu Alhassan
