Za ka yarda da manufar “kashin dankali”?

Daga BELLO WANG

Yau na ga wannan labari: Charles Onunaiju, wani masanin ilimin hulɗar ƙasa da ƙasa na Najeriya, ya ce asusun tarayyar Amurka na ci gaba da ƙara kuɗin ruwa, matakin da ke iya haifar da mummunan tasiri ga ƙasashe masu tasowa.

Don neman shawo kan matsalar hauhawar farashin kayayyaki, asusun tarayyar Amurka ya ƙara kuɗin ruwa har sau 6, tun farkon shekarar 2022.

Amma me ya sa matakin ya shafi sauran ƙasashe? Saboda wannan manufar za ta janyo dalar Amurka daga kasuwannin ƙasa da ƙasa, don su koma ƙasar Amurka.

Hakan kuma zai sa a dinga canza kuɗaɗen sauran ƙasashe zuwa dalar Amurka, lamarin da zai haddasa faɗuwar darajar kuɗaɗen, da hauhawar farashin kayayyaki a waɗannan ƙasashe, da ƙarancin dalar Amurka, da jarin waje a kasuwanninsu, gami da raguwar adadin kayayyakin da suke fitarwa zuwa ƙasashen waje.

Don tinkarar wannan mummunan tasiri, manyan bankunan sauran ƙasashe su ma sun daga kuɗin ruwa don neman kiyaye dalar Amurka a gida.

Misali, Babban Bankin Najeriya ya riga ya daga kuɗin ruwa zuwa 16.5%.

Sai dai manufar ba ta yi amfani sosai ba, ganin yadda darajar Naira na ci gaba da raguwa.

A sa’i ɗaya kuma, ƙaruwar kuɗin ruwa na haifar da ƙarin matsin lamba ga kamfanonin da suka ci bashi daga bankuna.

A cewar Charles Onunaiju, yanzu Nijeriya na fama da hauhawar farashin kayayyaki da matsalar ƙarancin dalar Amurka a kasuwa, da faɗuwar darajar kuɗin ƙasar da dai sauransu, galibi saboda yadda take fuskantar matsin lamba daga wasu manufofin ƙasashen ƙetare.

Kana Najeriya da sauran ƙasashe masu tasowa na fuskantar matsalolin raguwar guraben aikin yi, da ƙaruwar bashin da ake ci.

Ta wata manufarta kadai, kasar Amurka ta tura matsalolin hauhawar farashin kayayyaki, da koma bayan tattalin arziki, ga sauran kasashe, musamman ma ƙasashe masu tasowa.
Matakan “kashin dankali” mai kama da wannan, da ƙasar Amurka ta yi wa sauran ƙasashe, sun yi yawa.

Idan har mun ɗauki aminan ƙasar Amurka, wato ƙasashen Turai a matsayin misali.

Ta hanyar fakewa da maganar daidaita yanayin da ake ciki a nahiyar Turai a fannin tsaro, ƙasar Amurka ta mai da ƙasashen Turai ƙarƙashin jagorancinta.

Kana ta yi amfani da matsalar ƙarancin makamashin da ƙasashen Turai suke fuskanta wajen sayar musu da iskar gas mai tsada matuka.

Ban da wannan kuma, ƙasar Amurka ta ba da dimbin tallafi ga sana’ar kirkiro motoci masu amfani da lantarki ta ƙasar, don janyo masana’antun Turai zuwa gidanta. Ga shi, ƙasar ba ta kyautatawa aminanta, balle ma sauran ƙasashe.

A wannan zamanin da muke ciki, wata ƙasa kaɗai take samun dimbin tallafi daga ƙasar Amurka, wato ƙasar Ukraine.

Amma dalilin da ya sa haka, shi ne Amurka na yin amfani da Ukraine wajen raunana ƙasar Rasha.

An biya kuɗin, don sanya mutanen ƙasar Ukraine, maimakon na ƙasar Amurka zub da jini. Gaskiya Amurkawa suna da wayo.

Shafin yanar gizo ta Internet ta Modern Diplomacy, na Turai, ya ce kasar Amurka ƙasa ce dake son ƙwayar dukiyoyi daga sauran ƙasashe.

Ko da yake wata babbar ƙasa ce, amma za ka yarda da manufarta ta “kashin dankali”?