‘Yan Sama Jannati uku na ƙasar Sin za su yi aiki a kumbon Shenzhou-15

Daga CMG HAUSA

Ofishin kula da aikin binciken sararin samaniya na kumbo mai ɗauke da ‘yan sama jannati na ƙasar Sin ya bayyana cewa, ofishin ba da umurni na ayyukan kumbon binciken sararin samaniya na ƙasar Sin, ya tsaida ƙuduri cewa, ‘yan jannati uku wato Fei Junlong, da Deng Qingming, da Zhang Lu za su yi aiki a kumbon Shenzhou-15, ƙarƙashin jagorancin Fei Junlong.

Gobe Talata ne, za a harba kumbon Shenzhou-15 cikin sararin samaniya daga cibiyar harbar kumbona ta Jiuquan dake arewa maso yammacin ƙasar Sin.

Mai fassara: Zainab