Su waye Shuwa Arab (II)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A yau za mu cigaba da kawo wa masu karatu jarihin Shiwa Arab, kamar yadda mu ka fara a makon da ya gabata.

Amma Idda da Badejo (Babu Shekara) sun ayyana cewa, rayuwa kala uku suke yi saboda rabuwar su kashi uku; manoma da kuma makiyaya ko kuma waɗanda suka haɗa duka biyu. Makiyaya da manoma su ne mazauna ƙauyuka na dindin da kuma garuruwa na dinin. Waɗanda suka haɗa noma da kiwo kuma su suke irin waccar rayuwa ta tashi-mu-je-mu.

Zamantakewa:

Yanayin zamantakewar jama’ar Shuwa-Arab cike take da taimakekeniya. Suna rayuwa a irin salon nan na zuriya mai nisa wadda ake danganta mutum da kakaninsa har kusan kaka na shida. Bisa wannan dalilin ya zama suke da zuriya-zuriya ta zamantakewa waɗanda suke kaiwa ga kafa gari da sunan mutum guda. Jenkins (1996); Wikipedia (2020) sun ruwaito waɗannan dangi-dangi a matsayin zuriyoyin Shuwa Arab mafiya shahara: Bani Salim, Aulad Hamayd, Habbaniya, Hawazma, Missiriya, Bani Husayn (Zuriyar da fitaccen Malamin Hadisi, Sheikh Sharif Saleh AlHusaniy ya fito daga cikinta), Humr, Bahr al-Arab, Reizegat, Ta’aisha, Beni Helba, Beni Khuzam (Zuriyar da Sarkin Shuwa Arab na Lagos, Sultan Jibril Yahaya ya fito daga cikinta) da kuma Salamat. A tare da haka kuma, sun fito ne daga tushe ɗaya; wato dukkanin su zuriyar Juhaynah ne.

Suna rarraba ayyuka a tsakaninsu domin taimakon juna. Mata, maza, yara, kowa da aikin da ya ratayu a kansa wanda yake gudanarwa domin rayuwa ta tafi daidai. Barin mu shiga taskar Bethany World Prayer Center, (1997); Pray for the Nation, (2005), domin samun abin faɗa.

Maza: Alhakin kiwata shanu da sauran manyan dabbobi da kuma sayar da su da aikin gona domin samar da abincin da iyali za su ci yana kan iyaye maza.

Mata: Nauyin kula da yara da sauran harkokin gida da kuma tatsar nonon saniya da sayar da shi duk ya rataya a kan iyaye mata ƙari a kan gina ɗakunan kwana. Wannan kuɗi da suke samu daga sayar da nono da man shanu da shi suke cefanen gida har ma su samu abin da za su adana.

Yara: Yara maza suna taya iyaye maza aiki kamar kiwon ƙanan dabbobi da suka haɗa da ’yan maraƙa, awaki, tumaki da sauransu. Haka nan ma sukan je gona noma. Su kuma ’ya’ya mata suna taya iyaye mata aiki. Kamar irin su kai niƙa gari, sayar da nono a wasu lokutan, zaman jiran gida, sayo kayan haɗin abinci da sauransu.

Addini:

Jenkins (1096), ya ruwaito cewa dukkan Shuwa Arab Musulmi ne masu tsayar da salloli biyar a jam’i. Wasu daga cikin su sukan ziyarci hajji domin ibada. Ya kuma ce ba a san wani mabiyin addinin Kirista ba a cikin Baggara. Joshua Project (2020), sun bayyana cewa tun cikin ƙarni na goma sha uku suka karɓi addinin Musulunci (Wato yau suna da shekaru 820 kenan 1200 – 2020).

Qari a kan haka, sun bayar da gagarumar gudunmawa wajen tabbatuwar addinin Musulunci a yankin Afirka kamawa tun daga yaɗa shi har zuwa kare shi daga mahara a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso.

Jidda da Badejo (Babu Shekara), sun ruwaito cewa Shuwa-Arab suna da matuƙar tasiri a tsohuwar Daular Kanem Bornu, daular da suka bai wa gagarumar gudunmawa wajen kareta daga harin Fulani, Bulala, Bagirmi da Wadai. Wannan kuma saboda dangataka mai ƙarfi da ke tsakanin su da Kanurai sama da kowace ƙabila da ke yankin.

Jenkins (1996), ya bayyana cewa, Baggara, su ne tushen boren da Musulmi Mahadiyawa (Mahdist Muslim) suka yi wa Mulkin Turawan Ingila da haɗin guiwar Daular Othman (British-Ottoman rule) a ƙasar Sudan.

Wikipedia (2020), kuma suka ƙara da cewa su ne ƙashin bayan boren da Mahadiyawa suka yi wa mulkin Turkiya da Misira (Turko-Egypt rule) a shekarun 1880s, tare da cewa, mataimakin shugaban rundunar, Abdullahi ibn Muhammad shi ma Baggara ne da ya fito daga zuriyar Ta’aisha. Jenkins (1996), ya ci gaba da cewa daga baya kuma su suka zama ginshiƙai wajen jagoranci Daular Mahdiyawa bayan rasuwar jagoran Daular wato Mahdi.

Ya kuma ci gaba da zayyano gudunmawar da suka bayar wajen kafa sabuwar daula a ƙasar Etofiya (Ethiopia) a shekarar 1887 ta yadda har ta kai su ga samun nasarar kawar da sarkin Etofiya, Yohannes IV a shekarar 1889. Sun mamayi ƙasar Misira a shekarar 1889. Haka nan kuma ya ruwaito cewa sun kutsa ƙasar Iriteriya (Eretria) a cikin shekarar 1893 inda daga bisani Italiyawa suka samu galaba a kansu.

Karatu:

Shuwa-Arab suna saka ’ya’yansu a makaranta, duk da cewa, karatun ’ya’ya mata yakan tsaya ne daga shekaru shida, kamar yadda ya zo a ruwayar Bethany World Prayer Center, (1997); Pray for the Nation, (2005). Amma Jidda da Badejo (Babu Shekara) sun siffata su da mutane masu tarin ilimi.

Sutura:

Bethany World Prayer Center, (1997), sun ruwaito cewa, suturar Shuwa-Arab ita ke bayyana muhimmancin mutum a cikin jama’a. Maza suna saka doguwar riga ta auduga wadda ake kira da suna boubou. Shugabanni sukan naɗa shuɗi ko farin rawani wanda a nan ma girman rawanin ke bayyana iya girman matsayin wanda ya saka shi. Mazaje sukan rataya adda a kafaɗarsu tare da rataya layu a wuya, jirge a kafaɗa ko kuma guru a ƙugu.

Matan aure suna lulluve jikinsu ta hanyar naɗa mayafin da ke tashi daga kafaɗunsu, zuwa gangar jiki har ƙafa sannan ya lulluɓe kansu. Sannan kuma suna saka abin ƙafa, kambu, sarƙa da kuma ’yan kunnayen da ke ƙara musu kyau.

Fitattun Mutane:

A nan Nijeriya, ƙabilar Shuwa Arab suna da fitattun mutane ’yan ƙasa da suka haɗa da:

  • Marigayi Janar Mamman Shuwa, wanda ya jagoranci ɗaya daga cikin rundunonin da suka yi yaƙin basasa.
  • Alhaji Musa Dagash, sakataren gwamnatin Tarayyar Nijeriya a zamanin mulkin Sir Abubakar Tafawa Valewa.
  • Sheikh Jarma wanda ya taɓa zama gwamnan Borno.
  • Dakta Muhammad Abba Aji wanda ya tava zama ɗan Majalisar Dattawan Nijeriya.
  • Kanal Muhammad Yaqub.
  • Sheikh Sherfi Saleh Alhusainy, fitaccen masanin hadisi a duniya.
  • Hajiya Maryam Abacha, matar tsohon shugaban ƙasa marigayi Sani Abacha.
  • Babajidda, wanda yake jakadancin Nijeriya a Cana a yanzu haka.
  • Girema Muhammad, Babban ɗan kasuwa a Legas.
  • Alhaji Ahmad Girema, sarkin Abuja a zamanin mulkin marigayi Sani Abacha.
  • Sunusi Dagash, tsohon ministan sufuri na Nijeriya a zamanin gwamnatin shuagaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan.