2023: Buhari bai so Tinubu ba kuma bai yarda da Osinbajo ba – Lamiɗo

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamiɗo ya yi iƙirarin cewa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari bai goyi bayan yunƙurin Shugaba Tinubu ba na son zama shugaban Nijeriya kuma bai yarda da Mataimakinsa, Yemi Osinbajo ba.

Ya ce, a madadin haka sai Buhari ya nemi tsohon shugaban Majalisar Dattijai, Ahmed Lawan a matsayin wanda zai gaje shi.

Lamiɗo yace, Tinubu shi ya ingiza kansa wajen neman shugabancin Nijeriya kuma ya yi nasara ba tare da ubangida ba.

Tun kafin lokacin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC, Tinubu ya shelanta cewa, yanzu lokacinsa ne a yayin wani taro a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, don haka ne Buhari ya nuna halin ko-in-kula tare da zaɓar wani ɗan takarar.

Ya ƙara da cewa, bayan shekara takwas da ɗan Arewa ya yi a kan karagar, ba zai yiwu ba a sake yin wani shugaban ɗan yankin a Nijeriyar yau.

Sannan, rashin ƙarfafa wa ɗan takarar nasa gwiwa ya sanya Tinubu yin nasara a lokacin zaɓe fidda gwani.

Tsohon gwamnan ya kuma ce duk da ƙoƙarin daƙile damar Tinubu ta hanyar sauya fasalin Naira da ƙirƙirar ƙarancin man fetur, sai da Tinubu ya yi nasara daga baya.

By Babaji