
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Ɗan Majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Badagry a jihar Legas, Mista Sesi Whingah ya tabbatar wa al’ummar yankinsa cewa nan ba da jimawa ba za a buɗe iyakokin Nijeriya don gudanar da harkokin kasuwanci a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Tinubu.
A lokacin da ya ke magana a yayin wani taro na masu-ruwa-da-tsaki da matasa na yankin nasa wanda ofishinsa ya shirya, ɗan majalisar ya bayyana cewa buɗe iyakokin wani ɓangare ne na ƙoƙarin haɓaka adadin kuɗin haraji na gida da Nijeriya ke karɓa.
Ya ce, tsarin ya na da muhimmanci kuma zai taimaka wajen samar da sakamako mai kyau, ya na mai cewa gwamnati ta na sane da halin matsin rayuwa da al’umma ke ciki.
Ya ce a saboda haka ne za ta sake buɗe iyakokin don a samu sauƙin harkokin yau-da-kullum.
