2023: Ina da yaƙinin APC za ta lashe zaɓe – Adamu

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu ya ce, APC na da yaƙinin za ta lashe zaɓen 2023 wanda zai gudana cikin aminci da adalci.

Adamu ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Jadiyar Poland a Nijeriya, Joanna Tarnawska, a ofishinsada ke Abuja.

Ya ce, duba da irin goyon bayan ɗimbin ‘yan Nijeriya da APC ke da shi, babu yadda za a yi jam’iyyar ta sha kaye a zaɓen 2023.

Jakadiyar ta ziyarci Adamun ne bayan da jam’iyyarsa ta kammala zaɓen fidda gwani cikin nasara innda ta zabi dan takarar da zai yi mata takarar shugaban ƙasa a babban zaben 2023.

Ko kafin wannan lokaci Joanna Tarnawska, ta taya Adamu murnar zaɓensa da aka yi a matsayin Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa.

Da take jawabi yayin ziyarar, Joanna Tarnawska ta ce ƙasarta na matuƙar sha’awar cigaban da Nijeriya ke samu a fagen siyasa, ƙasar tata za ta so ganin an miƙa ragamar mulki cikin lumana bayan kammala wa’adin Buhari a shekara mai zuwa.

Haka nan, ta kira ga Jam’iyyar APC da ta samar wa mata da matasa damammaki don a dama da su a harkokin siyasar ƙasar.

Ta Poland na burin inganta ƙawance diflomasiyya tsakaninta da Nijeriya, musamman a fannin bunƙasa tattalin arzikin ƙasashen biyu.