2023: INEC ta wallafa sunayen ‘yan takarar da ta yarda da su daga kowacce jam’iyya

Daga AMINA YUSUF ALI

Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta wallafa bayanan wasu ‘yan takarar shugabancin Nijeriya da na majalisu waɗanda jam’iyyu suka tura wa hukumar a matsayin waɗanda za su wakilci jam’iyyun a kakar zaɓen ta 2023.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan bayani INEC ce ta wallafa shi ne a ranar Juma’ar da ta gabata a ofishinta na ƙasar nan.

Bayanan da ta wallafa game da ‘yan takarar sun haɗa da, Sunayen ‘yan takarar shugaban ƙasa da kowacce jam’iyya ta tsayar a matsayin ɗan takararta da abokan takararsa (mataimaki), sannan da ‘yan takararsu na ‘yan majalisar dattawa da kuma na majalisar wakilai.

A cikin bayanan akwai sunan ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu da abokin takararsa Malam Ibrahim Masari.

Hakazalika, akwai sunan Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasar nan na jam’iyyar PDP da abokin takararsa, Ifeanyi Okowa.

Sannan akwai Peter Obi, ɗan takarar shugabancin ƙasar nan a ƙarƙashin jam’iyyar LP, da mataimakinsa, Doyin Okupe; akwai kuma Osita Nnadi, ɗan takarar shugaban ƙasar a Jam’iyyar APP da mataimakinsa Isa Hamisu.

Sannan bayanin dai a ƙunshi sunan Abiola Kolawole, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasar a jam’iyyar PRP da abokin takararsa Ribi Marshal; Sai Rabiu Musa Kwankwaso, ɗan takarar shugaban qasa a jam’iyyar NNPP da abokin takararsa, Johnson Oladipupo.

Sauran sun haɗa da, Yabagi Sani, ɗan takarar shugaban ƙasar a ADP da mataimakinsa, Udo Okey -Okoro; Sai Ado-Ibrahim Abdulmalik, na jam’iyyar YPP da mataimakinsa, Enyinna Kasarachi.

Hakazalika a dai cikin wallafar ta INEC, akwai sunayen Omoyele Sowere na AAC, da mataimakinsa, Garba Magashi; sai Mamman Dantalle, na jam’iyyar APM da abokin takararsa, Ojei Princess; sai Chukwudi Umeadi ɗan takarar jam’iyyar APGA da mataimakinsa, Koli Mohammed.

Haka nan akwai sunayen Oluwafemi Adenuga, halastaccen ɗan takara na jam’iyyar BP, da mataimakinsa Turaku Mustapha; Sai Daberechukwu Nwanyanwu, na jam’iyyar Zenith Labour Party (ZLP), da mataimakinsa, Ramalan Abubakar; Sannan akwai Dumebi Kachikwu ɗan takarar jam’iyyar ADC da abokin takararsa, Ahmed Mani.

Sannan a ƙarshe akwai sunayen Hamza Almustafa, ɗan takarar shugaban ƙasar a jam’iyyar AA da mataimakinsa Chukwuka Johnson.