Super Eagles ta koma matsayi na 31 a jadawalin FIFA

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta koma matsayi na 31 a sabon jadawalin FIFA da aka fitar a ranar Alhamis.

An buga sabon matsayi na ne akan gidan yanar gizon FIFA.

A Afirka, Super Eagles yanzu ta koma matsayi na huɗu bayan Senegal da Morocco da Tunisia, waɗanda ke matsayi na ɗaya da na biyu da na uku.

Saliyo wadda ta yi rashin nasara a hannun Eagles a wasannin neman cancantar shiga gasar AFCON ta 2023, ta koma mataki na 113 yayin da Guinea-Bissau ta kasance a matsayi na 115.

Sao Tome and Principe, wacce ta sha kashi a hannun Eagles da ci 10-0 a wasannin neman gurbin shiga gasar AFCON, ta koma matsayi na 187.

A halin da ake ciki, Brazil ta ci gaba da zama a matsayi na ɗaya sannan Belgium ma ta riƙe matsayi na biyu.

Argentina ta koma daga matsayi ɗaya zuwa na uku, inda ta maye gurbin Faransa da ke matsayi na huɗu, ita kuma Ingila ba ta taka leda a matsayi na biyar.

Spain tana matsayi na shida, Italiya ta bakwai, Netherlands a takwas, Portugal a matsayi na tara kuma a lamba 10 Denmark ce.

Za a buga Matsayin Duniya na FIFA na gaba a ranar 25 ga Agusta 2022.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *