2023: Su waye matan da ke zawarcin kujerar gwamna a jihohin Nijeriya?

Daga AISHA ASAS

Ɗaya daga cikin dama da ‘yancin da dokar Nijeriya ta bai wa mata akwai damar riƙe madafun iko, wato fitowa takara ta kowanne ɓangare, babba da ƙaramin muƙamai, tun daga shugaban ƙasa har zuwa kansiloli. Wannan ne ya sa jajirtattun mata da dama suka yi yunƙurin ɗarewa ɗaya daga cikin kujerun da za su ba su damar baje irin ta su hikima ta hanyar juya sitarin wani vangare na wannan ƙasar ko ƙasar bakiɗaya.

Ba ɓoyayyen abu ba ne irin yunƙurowar da mata suka yi kan sha’anin da ya jivinci siyasa, sun sanya jajircewa da zata sa mai adalci amincewa sun shirya tsaf don bada gudunmawa a gyaran matsalolin ƙasar nan.
Duk da cewa babu wata doka da ta iyakance wa mata muƙaman da za su iya tsayawa takara, sai dai hakan bai hana maza yin babakere su hanasu rawar gaban hantsu a siyasa, wataƙila hakan bai rasa nasaba da zamewar mata barazana gare su, dalilin yawan su da ya zarta na mazan, idan matan suka samu sakewa, akwai yiwar hula ta koma bin ɗankwali a harkar siyasar Nijeriya.


Ta iya yiwa wannan ne ya sa suke amfani da ƙarfin ikonsu wurin danne matan su hana su motsi, ta hanyar hana su kataɓus a sha’anin siyasa, har su gaji su gudu don ba su da wata mafita.

Mai karatu zai iya yarda da wannan rubutun idan ya yi duba da su waye ke riƙe da manyan muƙamai na siyasa, kuma idan ya tambaye kansa ko matan basa yin yunƙurin neman manyan muƙaman ne, kuma sun taɓa kai labari?

Mata da yawa a harkar siyasa sun sha ƙorafin tauye su da ake yi tare da nuna masu ba su isa ga takarar ba ko da kuwa mutane na son su, ba kuma don komai ba sai don kasancewar su mata. Wannan na ɗaya daga cikin dalilin da ke sa mata da yawa musamman a Arewacin Nijeriya ba su cika dogon ƙarko cikin sha’anin siyasa ba matuƙar muƙaman ne suke hari ba ‘yan abi yarima a sha kiɗa ba.

Maganganu da dama ana amfani da su wurin jifar takara mace da ɗanyen kashi, don ganin ba a ba su dama irin wadda dokar ƙasa ta tanada ba. Wasu kan yi amfani da addini, yayin da wasu kan sako al’ada a gaba a yayin da suka ɗauko zancen rashin dacewar mace a matsayin shugaba ga al’umma. Sai dai suna yi masu abinda suka kira da adalci ta hanyar ba su wasu muƙamai da za su iya bada gudunmuwarsu, kamar mai bada shawara, ministoci da sauran su.

Duk da wannan ƙalubale da mata ke fuskata a harkar siyasa bai hana wasu daga cikin jajirtattu a cikin jajirtattun matan tsayawa tsayin daka, su jure duk wata sara da suka a tafiyar don ƙudurinsu na ganin sun kai inda za a ture wa Buzu naɗi.

Duk da cewa, ba za a iya cewa mata basa riƙe muƙamai a siyasa ba, domin da dama sun samu zama ‘yan majalisu, ciyamomi da makamata su, sai dai har yau ba a tava samun mace a Nijeriya da ta yi sanar zama gwamna ko shugabar ƙasa ba, duk da cewa wannan ya zama ruwan dare a wasu ƙasashen da suka cigaba, kuma suka zama allon duba ga ƙasashe irin Nijeriya. Kuma hakan ba fa yana nufin matan ba sa yin yunƙurin fitowa a muƙaman ba ne, sai dai ba su cika samun damar kai labari. Tun daga rashin samun damar tsayar da su a manyan jam’iyyun da ke da ƙarfi da faɗa a ji a Nijeriya ne ƙudurin na su zai samu tazgaro, daga nan kuma sai labarin ya zama tarihi.

Sai dai ga dukkan alamu zaɓe mai zuwa zata iya sauya zani a tafiyar siyasar mata a Nijeriya, duba da damar tsallake matakin farko da wasu matan suka samu a wannan karo da a baya ba a samu irin su ba. Abin nufi, wasu matan sun samu nasarar lashe zaɓen fidda gwani na ‘yan takarar gwamna a wasu sanannun jam’iyyu irin su APC, LP da sauran su, wanda kansu ne wannan darasi na wannan sati ya samu tushe. 

Mata da dama shekaru mabambanta sun nuna kwaɗayinsu ga samun gujerar gwamna a jihohi da dama a Nijeriya, sai dai waɗanda ke samun nasarar lashe zaven fida gwani a wannan matsayi sun tsaya a iya jam’iyyu masu tasowa, waɗanda ba su cika tasiri ba. 
Darasin namu na yau zai kawo wa masu karatu jerin sunanyen matan da suka yi nasarar samun damar tsayawa takarar gwamna da kuma jihohin da suka fito:

Sanata Aishatu Dahiru Ahmad (Binani):

Ɗaya daga cikin matan da suka tsallake wannan matakin akwai Aishatu Dahiru Ahmad, wadda aka fi sani da Binani. Sanata ce mai waƙiltar Adamawa ta Tsakiya, kuma ɗaya daga cikin ‘yan kwamitin kula da sha’anin muradun ƙarni. ‘Yar takarar gwamna ce a ƙarƙashin jam’iyya mai mulki, wato Jam’iyyar APC.

Binani ta yi nasarar kayar da abokin takarar ta na kusa Nuhu Ribadu, tsohon shugaban hukumar EFCC da ƙuri’u 430, yayin da yake da ƙuri’u 288.

Duba da ƙwarewa tare da gogewarta a siyasa ne ya sa ake hasashen zata iya kawo nasara a jam’iyyar ta hanyar kayan da gwamna mai ci Ahmad Fintiri, wanda ya fito daga jam’iyyar adawa, wato PDP. Ga kuma uwa uba fitowarta daga jam’iyya mai ci a yanzu.

Beatrice Itubo:

Beatrice Itubo wadda ta kasance shugabar Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya, ta samu nasarar zama ‘yar takarar gwamna a Jihar Rivers a ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar LP, wadda ta kasance jam’iyyar da ake hasashen zata lashe zaɓe a ɓangarorin Inyamurai a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa, wadda ta tsayar da Peter Obi.

Yayin bayyana sakamakon zaɓen, an tabbatar da Itubo a matsayin ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar dalilin ƙuri’un da ta samu da suka zarta na abokin takaranta na kusa, wato Mista Dienye Braide, inda ta samu ƙuri’u 201, yayin da Mista Dienye ke da 71.

Beatrice Itubo ta yi alƙawarin ba zata ba wa jam’iyyar tasu kunya ba, kuma ta yi alwashin ciyar da Jihar Rivers gaba, ta hanyar samar da zaman lafiya da kuma kawar da rashin tsaro da ya adabi jihar. Ta yi wannan bayayin ne yayin da ta ke amsa tambayoyin manema labarai, jim kaɗan bayan kamala taron zaɓen.
Duba da yanayin amon da ɗan takarar shugaban ƙasa a wannan jam’iyyar ya yi a faɗin ƙasar nan, mutane da dama suna hasashen zai iya yiwa Beatrice Itubo ta kai labari a zaven 2023.

Sophia Cookey:

An tsayar da Sophia Cookey a ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar ZLP, wato Zenith Labour Party a matsayin ‘yar takarar gwamnar Jihar Rivers, ma’ana dai zata zama ɗaya daga cikin abokan karawar Beatrice Itubo a zaɓe mai zuwa. Duk da cewa jam’iyyar bata yi ƙarfin waɗanda aka lissafa a baya ba, ba zai hana Sophia zama cikin jerin waɗanda ake wa kyakyawan zato a zaɓe mai zuwa, duba da irin rawar da ta ke takawa a tsakanin mutanenta da irin soyayyar da suke bayana wa gare ta.

Obiang Marikane Stanley:

‘Yar takarar gwamnar Jihar Cross Rivers a ƙarƙashin Jam’iyyar ADP, wato Action Democratic Party, Obiang Marikane Stanley na ɗaya daga cikin jerin lissafin matan da ake tunanin su kawo sauyi a siyasar Nijeriya, ta hanyar kafa tarihin da ba a taɓa gani a siyasar Nijeriya.

Nnana Lancaster Okoro:

Ƙwarariyyar lauya da ke da tabbacin zata ci kujerar gwamnar Jihar Abia a zaɓe mai zuwa, sakamakon yaƙini da ta ke da shi na cewa, ubangijinta ya aiko ta ga mutanen Abia don ta kawo masu sauqi a cikin matsi, ta kuma sauya masu yanayin rayuwarsu. 

Nnana ta yi iƙirarin cewa ta san ba zata yi kunya ba, saboda bata da ja ga hukuncin na ubangijinta. A cewar ta, lokaci ya yi da ya kamata al’ummar Abia su ba wa mata dama don su gwada masu tasu iyarwa, kuma ta yi alƙawarin ba zata ba su kunya ba.

Okoro ta nuna takaicinta kan yadda ake mayar da mata baya a sha’anin siyasa, alhali suna da rawar da za su iya takawa. Ta kuma yi kira da Jihar Abia ta canza tafiyar da ta ke yi kan sha’anin zaɓe ta hanyar ba wa mata dama su riƙe madafun iko a yanzu, saɓanin baya da ta ce babu mace ko ɗaya a ‘yan majalisun jiha da suke da su.

Khadijat Abdullahi Iya:

Khadijat Abdullahi Iya ‘yar takarar gwamna ce a Jihar Niger a ƙarƙashin Jam’iyyar APGA, wato All Progressives Grand Alliance. ‘yar siyasa ce da ta jima ana gwagwarmaya da ita. Ko a zaɓen 2019, Khadijat Abdullahi Iya ta fito takara a ƙarƙashin inuwar ANN a matsayin mataimakiyar shugaban ƙasa.

Honarabul Ngozi Ogbuleke:

‘Yar takarar gwamna a ƙarƙashin Jam’iyyar SDP a Jihar Abia, Honarabul Ngozi Ogbuleke, ‘yar siyasa ce ta ƙwarai da ake kyautata zaton zata iya samun ƙuri’un mutane da dama, duk da raunin jam’iyyar da ta tsaya a ƙarƙashinta.

Tina Barde:

‘Yar takarar gwamna ce da zata kara da Khadija Abdullahi Iya a zaɓe mai zuwa a ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar LP, wato dai a Jihar Niger. Kamar yadda muka faɗa a baya, duk da zamewar Jam’iyyar LP mai tasowa ta samu tagomashi a wurare da dama albarkacin sunan ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar, wato Peter Obi.

Kassim Jackie-Adunni:

Jam’iyyar NNPP ta tsayar da Dakta Kassim Jackie-Adunni a matsayin ‘yar takarar gwamna a Jihar Ogun. Basarakiya ce da ke riƙe da sarautar Jagunmolu Iyalode ta Birnin Igbore, kuma Iyalaje ta Sango-ota, sannan kuma Yeye Loro ta Masarautar Akinwale Owu. ‘Yar siyasa da ta taka muhimmiyar rawa a rayuwar mutanenta, musamman ɓangaren ilimin yara. Baya ga haka, a zaven da ya wuce ma ta tsaya takara a ƙarƙashin Jam’iyyar UDP.

Sufiat Adekemi Iskil-Ogunyomi:

Jihar Ogun na ɗaya daga cikin jihohin da aka samu ‘yan takarar gwamna mata fiye da ɗaya. Sufiat na ɗaya daga cikin matan da za su samu isa babban zaɓe mai zuwa a matsayin ‘yar takarar gwamna a ƙarƙashin Jam’iyyar AA.

Jam’iyyar AA dai za a iya kiranta da sabuwar jami’iyya, sai dai hakan bai zama abin sare gwiwa ga ‘yar takarar ba, dalilin amincewa da suka yi cewa, zaɓe mai zuwa zata canza zane, domin rana ta fito duhu ya gushe, wato kai ya waye game da cancanta da kuma alfanun zaɓen mata a matsayin shuwagabanni. 

Don haka ba abinda za mu ce sai dai Allah Ya ba mu sadakar yawancin rai, mu ga ko za ta iya sauya zane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *