2023: Ya kamata matasa su guje wa shiga bangar siyasa – Ƙungiyar Ushaƙun

Spread the love

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe

Ganin yadda babban zaɓe ya ke ƙara ƙaratowa kuma ’yan siyasa kan yi amfani da matasa wajen aika-aika irin na bangar siyasa, ƙungiyar Ushaqun Nabiyi Rasulul a’azam ta yi kira ga iyayen yara da su kula da ‘ya’yan su.

Kiran hakan ya fito ne ta bakin shugaban ƙungiyar ta Ushaqun Nabiyi na ƙasa Sherif Auwal Siddi Bolari, a lokacin da ƙungiyar ta gudanar da babban taron ta a Gombe.

Ushagun Nabiyi ƙungiya ce ta mawaƙan ƙasidun Hausa ta Nijeriya ƙarƙashin jagoranci Shugabanta na ƙasa, Sheriff Auwal Siddi Bolari, inda ya ce, matasa su hanu da duk wani abu da zai iya kawo tsaiko ga zaman lafiya da tsaro a jihar da ƙasa baki ɗaya.

Ya ƙara da cewa, dole ne iyaye su sanya ido sosai kan ’ya’yansu su kare su daga shiga hatsaniyar siyasa, yana mai jaddada cewar majalisar ta umarci mambobinta a faɗin ƙasar nan su riƙa rubuta ƙasidu da za su ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kan al’umma.

Ya kuma buƙaci ’yan siyasan su riƙa tallafa wa matasan a hanyar neman ilimi da ba su tallafin sana’o’i don dogaro da kai.

Sai ya sake yin kira ga matasa su tabbatar sun mallaki katin zaɓen su na dindindin wato PVC don zaɓen ‘yan takaran da su ke so a 2023.

Sheriff Auwal Bolari, ya ƙara da cewa, shirye-shiryen majalisar sun yi nisa na bikin sabuwar shekarar Musulunci mai zuwa, inda za a gudanar da abubuwa daban-daban ta yadda bikin zai fi na baya armashi da kayatuwa.

A nasa ɓangaren, uba a majalisar, Ahmad Musa Muhammad Sahibul Khairati, yabawa malaman addinin Musulunci ya yi bisa yadda suka gudanar da tafsiran Ƙur’ani mai girma a watan Ramadan da ya ƙare, dama irin addu’o’in da suka yi na neman zaman lafiya da tsaro ga ƙasa baki ɗaya.

Sahibul Khairati ya yi kira ga malamai da sauran al’umma su ƙara zage damtse wajen addu’ar Allah ya zaɓa mana ‘yan takara mafiya alkhairi a mukamai daban-daban a zaɓen 2023.

By Editor