2024: Gwamnan Jigawa ya gabatar wa majalisa kasafin N298.14bn

Spread the love

Daga ABUBAKAR MUHAMMAD TAHEER

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Umar Namadi Ɗan Modi, ya gabatar da kasafin shekarar 2024 ga ‘yan majalisar dokokin jihar a ranar Talata.

Namadi ya bayyana cewa kasafin na 2024, za a kashe Naira biliyan 111.98 wajen gudanar da ayyukan yau da kullum.

Haka kuma, ya ce an ware kashi 59% cikin 100% wanda adadin sa ya kai Naira biliyan 175.42 domin gudanar da manyan ayyuka a faɗin jihar.

Ya ƙara da cewa an yi nazari da taka-tsan-tsan wajen tsara kasafin duba da yadda Dalar Amurka take tashin gwauron zabbi da kuma farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.

Kaxalika, ya ce kaso 27.4 na kasafin za a kashe su wajen inganta rayuwar al’ummar jihar, sannan kuma akwai ayyuka gina gidaje a manyan garuruwan Hadejia, Birnin Kudu, Gumel, Kazaure, Rungume, Kafin Hausa da Babura wanda zai laƙume Naira biliyan 2.78.

Namadi ya ce inganta kiwon lafiya zai laƙume biliyan 20.3 wanda za a ɗaukaka darajar asibitoci 13 a wasu garuruwan jihar tare da maida biyu daga cikinsu manyan asibitoci.

Kasafin ya nuna ɓangarorin ilimi da noma da ruwan sha a ƙauyuka sun samu kaso mai tsoka inda Gwamna ya bayyana cewa za a ɗauki malaman makaranta 30,000 aiki a fadin jihar domin inganta sha’anin ilimi.

Kasafin na bana an masa take da “Kasafin kai jihar Jigawa tudun mun tsira”, ya ɗara ta bara saboda saboda ƙarin kuɗaɗen albashin ma’aikata.

By Editor