NLC, TUC sun dakatar da yajin aiki

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) da Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa ta Nijeriya (TUC) da sauran takwarorinsu, sun dakatar da yajin aikin da suka fara tun ran 14 gs Nuwamban 2023.

Dakatar da yajin aikin ya biyo bayan ganawar da ƙungiyoyin suka yi da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Lamarin Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu.

Taron wanda ya gudana a ofishin NSA ya samu halartar Shugaban TUC, Festus Osifo; Babban Sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja; Ministan Ƙwadago, Simon Lalong da sauransu.

NLC ta shiga yajin aiki ne don nuna rashin jin daɗinta kan dukan da aka yi ws shugabanta na ƙasa, Joe Ajaero a jihar Imo, tare da buƙatar dole a kamo waɗanda ke da hannu a badaƙalar don su fuskanci hukunci.