Tarihin Gidan Arewa a Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gidan tarihi na Arewa (Arewa House Centre For Historical Research and Documentation) da ke garin Kaduna a yankin arewa maso yammacin Nijeriya, cibiya ce da ke tattara tarihin Marigayi Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da Lardin Arewa da kuma tarihi da al’adu da sana’o’in yankin.

An kafa cibiyar ne bayan kisan gillar da aka yi wa Firimiyan Arewa na farko Sardauna, a juyin mulkin da sojoji suka yi a Ranar 15 Ga Watan janairun shekarar alif 1966. Sojojin sun tayar da bam, suka kuma kashe Sardauna da matarsa da ma’aikatansa a wannan gida. A juyin mulkin ne aka kashe Firaministan Nijeriya na farko Abubakar Tafawa-Balewa. Yanzu Gidan Arewa, wanda shi ne asalin gidan Sardauna, shi ne Cibiyar Bincike da Adana Tarihi na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya, Najeriya

Asali da tarihi:

“Gidan hukuma ne da aka mayar gidan tarihi domin tunawa da rayuwar Sardauna da mazajen ƙwarai da aka yi a lokacinsa,” inji Rabi’u Isah Hassan, Mataimakin Shugaban Gidan Tarihi na Cibiyar. A shekarar alif 1970 ne cibiyar ta fara aiki domin kiyaye tarihin Arewacin Nijeriya da shugabannin da suka kafa yankin.

Cibiyar na da nufin bai wa masu tasowa damar ganin yadda yankin ya zauna a dunƙule har zuwa sanda aka raba shi Jihohi shida a Zamanin Mulkin Janar Yakubu Gawon A Ranar 28 Ga Watan Mayu alif 1967. An fara gina gidan Sardauna ne a shekarun alif 1950 a matsayin gidan gwamnati na Firimiyan Arewa wato Alhaji Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato.

A zamanin Sardauna ma an yi wani shiri na musamman kan tattali da adana tarihin Arewa, ƙarƙashin wani masani ɗan ƙasar Ingila, Farfesa HFC Smith, wanda ya duƙufa wurin tattarowa da rubuta tarihin yankin. Gabanin kammala aikin ne aka yi juyin mulkin 1966, abin da ya kawo tsaiko, kafin daga baya a cigaba da aikin.

Wane ne ya mallaki gidan Arewa?

Bayan an raba Jihar Arewa zuwa jiha shida, an kafa hukumar kula da hidimomin da ƙadarorin da jihohin suka gada daga tsohuwar jihar Arewa. Ƙadarorin sun haɗa da Jami’ar ABU wadda ta ci gaba da zama ƙarƙashin jihohin har zuwa sanda Shugaba Murtala Muhammad ya mayar da ita mallakin gwamnatin tarayya a Alif 1976. A ƙarƙashin hukumar ne aka kafa Gidan Arewa a alif 1970, domin cigaba da aikin adana tarihin da aka riga aka faro a baya.

“Don haka sai magabata suka sa Gidan Arewa a ƙarƙashin Jami’ar ABU, kuma har yanzu aƙarƙashin jami’ar ta ke.”

Ayyukan farko:

A shekara 10 na farkon Gidan Arewa, Daraktan cibiyar na farko kuma ma’aikacin Sashen Tarihi na ABU, “ya horas da malamai ko ɗaliban tarihi da ko wanne aka ba shi fannin da zai qware a kai, musamman ma yankuna ko lardunan da suka fito.” Smith ya kuma jagoranci buga ayyukan tarihin Arewa kuma har yanzu a kan wannan baka ake.

Dalilin kafa gidan Arewa a gidan Sardauna:

An mayar da gidan Sardauna zuwa gidan tarihi ne saboda muhimmancinsa a matsayin gidan gwamnatin Arewa, da nufin nuna wa na baya yadda shugabanni na gari suka rayu da irin ayyukan alheri da suka yi wa Arewa. Sunan unguwar da gidan yake a wancan lokaci Nasarawa ko Unguwar Ministoci saboda a nan ministocin Arewa da aka fara yi suke zama.

A unguwar ce kuma aka yi gidajen da wakilan lardunan Arewa 12 suke zama idan suka zo halartar zaman Majalisar Arewa a Kaduna, bayan fara siyasa a Nijeriya a alif 1954. Ministoci da Sardauna a matsayinsa na Firimiya sun ci gaba da zama a rukunin gidajen.

Sardauna ya cigaba da zama a gidan har daren Juma’a wayewar garin Asabar 15 ga watan Janairu 1966, da aka yi juyin mulki. “A nan ya rasa ransa tare da mai ɗakinsa Hafsatu ‘yar Sarkin Musulmi Abubakar Na Uku da wasu barorinsa.”

Me ya sa ake ce masa Gidan Arewa?

An ba cibiyar suna Gidan Arewa ne domin ta kasance gida ga duk mutumin yankin ko mai nasaba da ita, duk da cewa an ƙirƙiri jihohi daga asalin jihar Arewa. “Amfanin tarihi shi ne ya nuna inda aka yi tarayya. Haɗin kan da ke tsakanin jama’ar Arewa ne ya sa aka ce masa ‘Gidan Arewa’.”

Abubuwan Tarihi:

Kayan tarihin da ke wannan cibiya sai wanda ya gani.

Wurin da aka kashe Sardauna.

Daga cikin abubuwan tarihi da ke Gidan Arewa akwai ‘inda aka samu gawar Sardauna, wanda yanzu aka killace domin nuna alama.

“Ba a cikin gidan aka binne shi ba, saboda a lokacin an sa dokar hana fita a faɗin Arewa.

“Sai dai aka kira Sarkin Musulmi na wancan lokaci, Abubakar III, aka gaya masa halin da ake ciki. Shi kuma ya ba da izini a rufe Sardauna a gidansa da ke Unguwar Sarki.”

Kayan Sardauna.

A cikin falon Sardauna Akwai agogonsa da darduma da carbi da littafin addini. Akwai kuma lasisin tuƙi da makullin alfarma da Hukumar Kula da Gidaje ta ba shi a lokacin bikin buɗe Babban Bankin Nijeriya (CBN).

Mun kuma ga hotuna da rediyo mai batir da kujeru da teburin tsakar ɗaki da matashi da sauran kayansa ciki har da manya rigunansa.

Ofishin Sardauna.

Har yanzu ofishin da Sardauna ya gina mai suna ‘Marble Office’, a gidan gwamnati na Gidan Arewa. Yanzu ‘Marble Office’, shi ne ofishin shugaban cibiyar.

Teburin Sardauna.

Teburin da ke ofishin Sardauna na nan har yanzu, ɗauke da kundayen gudanar da gwamnati. Teburin na cikin babban zauren kayan tarihin cibiyar.

Filin Wasa.

Har yanzu filin wasan ‘Fives’ da Sardauna ya yi na wurin da aka fara kafa shi a bayan gidansa, jama’a suna amfani da shi.

Kayan gargajiya.

A cikin zauren akwai kayan tarihi da na gargajiyar Arewa da na ɗaiɗaikun jihohi.

Sassan da ke Gidan Arewa.

Sassan Cibiyar Bincike da Adana Tarihi ta Arewa sun haxa da:

Gidajen Tarihi

Matattarar kayan tarihi da hotuna da kayan sana’a da kuɗaɗe da suturu da kayan amfanin magabata. Gidan tarihi na farko da ke Gidan Arewa shi ne gidan da Sardauna ya zauna. Bayan sojojin da suka yi juyin mulkin sun ƙona rufin gidan, daga baya an gyara shi, aka mayar da rufin sannan aka mayar da abubuwan da suka ƙone yadda suke.

Na biyu shi ne gidan tarihin jihohin Arewa 19 da baje-kolin yadda aka samar da yankin Arewa daga lokacin Turawa a alif 1900 har zuwa sadda aka yi juyin mulkin alif 1966.

Gidan tarihin jihohin Arewan na da babban zauren kayan tarihin jihar Arewa. Akwai kuma qananan zauruka da aka ware na al’adu da sarakuna da arzikin da Allah Ya hore wa ɗaiɗaikun jihohin yankin.

Kasancewar an ƙaddamar da zaurukan ne a alif 1995 kafin jihohin yankin su zama 19, ya sa kayan tarihin wasu jihohin yin tarayya a zaure guda, bayan an qara jiha uku a yankin a 1996.

Wasu ɓangarorin Gidan Arewa sun haɗa da:
ɗakin taro

Bayan karamin ɗakin taron da ke kusa da ofishin Sardauna a zamaninsa, an gina wasu manyan ɗakuna da zaurukan taro a Gidan, “domin cibiyar ta zama mahaɗa ta musayar ra’ayi da ilimi ta Arewa.”