Daga BASHIR ISAH
Gwamnatin Taryya ta ce a halin da ake cike ta samu nasarar tsare waɗanda Shugaban NLC na ƙasa, Joe Ajaero, ya ci na-jaki a hannusu, don haka ta ce tana bai wa ƙungiyar haƙuri kan ta dubi Allah ta janye yajin aikin da take yi.
Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Sha’anin Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, shi ne ya tabbatar da tsare waɗanda lamarin ya shafa wanda ake zargin ‘yan bangan siyasa ne.
MANHAJA ta rawaito an farmaki shugaban NLC ɗin ne a Owerri, babban birnin Jihar Imo, a ranar 1 ga Nuwamban 2023, a lokacin da ma’aikata a jihar suke zanga-zanga kan rashin biyan albashi.
Daga bisani ne NLC da TUC suka tsunduma yajin aiki inda suka buƙaci dole a kamo waɗanda ke da hannu wajen lakaɗa wa Ajaero duka.
Tuni dai harkokin kasuwanci suka gamu da cikas a sassan ƙasa sakamakon yajin aikin wanda NLC ta fara a ranar 14 ga Nuwamba.
Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba ta bakin Zakari U Mijinyawa, Ribaɗu ya yi kira ga ƙungiyar ta ƙwadago da ta dubi Allah ta dakatar da yajin aikin da ta tsunduma.
Ya bada tabbacin an tsare wasu da ake da zargi da hannu a badaƙalar, tare da cewa nan ba da jimawa ba za a bayyana sakamakon binciken ga al’umma.
