CBN ya shure wa’adin daina amfani da tsoffin takardun Naira

Daga BASHIR ISAH

Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya tsawaita wa’adin amfani da tsaffin takardun Naira, N200, N500 da kuma N1,000 har illa ma sha’a.

Daraktan sashen sadarwar bankin, Isa AbdulMumin, shi ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar ranar Talata mai taken, “CBN zai bada damar ci gaba da amfanin da tsaffin takardun Naira a dokance.”

Sanarwar ta ce an ɗauki wannan mataki ne daidai da yadda hada-hadar kuɗaɗe ke gudana a ƙasashen duniya.

Idan za a iya tunawa, a Oktoban 2022 ne CBN ya ƙaddamar da sabbin takardun kuɗi na N200, N500 da N1000, sannan ya yanka wa’adin da tsoffin takardun kuɗin za su daina aiki.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Dukkanin takardun kuɗin da Babban Bakin Nijeriya ya fitar daidai da Sashe 20(5) na Dokar CBN ta 2007, za su ci gaba da amfani har gaba da wa’adin 31 ga Disamban 2023 da aka gindaya a baya.

“Kuma CBN na aiki tare da hukumomin da suka dace domin kore hukuncin da kotu ta yanke kan batun.

“Kazalika, dukkanin rassan CBN da ke faɗin ƙasa za su ci gaba da bayarwa da kuma karɓar dukkan takardun kuɗin Nijeriya, tsoffi da sabbin.

“Don haka jama’a su ci gaba da amfani da dukkan takardun Naira (tsoffi da sabbi) a harkokinsu na yau da kullum tare da kulawa domin kare takardun kuɗin daga lalacewa,” in ji sanarwar.