
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar APC ta fitar da jaddawalin lokuta da tsare-tsaren gudanar harkokinta na babban zaɓen 2027, inda ta bayyana tsarin da za ta bi wajen yin zaɓukan fidda gwani a watan Mayu, 2026.
Haka kuma, ta ce za a yi zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa a ranakun 15 da 16 na Mayun 2026 a matsayin wani gagarumin ɓangaren ayyukanta.
Sakataren Shirye-shirye na Ƙasa na jam’iyyar, Sulaiman Argungu ne ya sanya wa takardar hannu, inda ya yi cikakken bayani akan fitarwa da sayar da tikitin tsaya wa takara, tantance ‘yan takara, wallafa sakamako, ƙorafi da kuma gudanar da dukkan zaɓukan fidda gwani na kowane ofishi.
A cewar jam’iyyar, ta fitar da jaddawalin ne bisa biyayya ga sharaɗin dokar zaɓe ta 2026 a ƙarƙashin kundin dokar ƙasa ta 1999 da aka gyara da kuma sharuɗɗan Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC.
APC ta bayyana cewa, ta ɗauki matakin ne domin tabbatar an gudanar da zaɓukan bisa gaskiya da adalci da ƙarfafa martabar dimukraɗiyya acikin jam’iyyar da kuma tabbatar da cikakken shiri ga zaɓen 2027.
Ga jaddawalin kamar yadda jam’iyyar ta fitar:

