
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta ƙara wa’adi ga jam’iyyun siyasa na su ɗora sunayen ‘yan takararsu na kujerun gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi daga ranar 8 zuwa 11 ga watan Agusta, 2026 yayin cigaba da shirye-shiryen zaɓen 2027.
INEC ta sanar da haka ne a wata takarda da ta fitar a ranar Lahadi ta hannun Shugabanta na Kwamitin ‘Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Zaɓe, Mohammed Haruna.
A cewarta, matakin ya biyo bayan magiya da ta samu daga ɓangaren jam’iyyun na a ƙara wa’adin domin su samu damar kammala ayyukan ɗora sunayen ‘yan takarar nasu baki ɗaya.
Da fari, an tsara jaddawalin ayyukan babban zaɓen 2027 ne ta yadda za a rufe karɓar sunayen ‘yan takara a ranar Asabar, 8 ga Agusta, 2026, amma a yanzu ta mayar da shi 11 ga wata don bai wa jam’iyyun damar kammala aikin cikin tsanake.
A wani labarin kuwa, INEC ta sanar da dakatar da aikin bayarwa da karɓar katin zaɓe (PVC) a Jihar Osun gabanin zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 15 ga Agusta.
Mohammed Haruna ya ce, masu zaɓe da suka nemi a sauya musu kati sakamakon dameji ko ɓata, an ba su damar ciro sabo daga na’ura har zuwa tsakiyar dare na ranar 9 ga Agusta.
Ya bayyana cewa, an ɗauki wannan mataki ne da nufin ba wa ‘yan ƙananan hukumomin Odo-Otin da Ife ta Tsakiya damar samun sabbin katina sakamakon sace nasu da wasu ɓata-gari suka yi a cibiyoyin karɓa guda biyu da ke jihar.
