Daga JOHN D. WADA a Lafia
Ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Jihar Nasarawa Dakta David Emmanuel Ombugadu ya yi alƙawarin magance matsalar tsaro da kuma ba da fifiko ga cigaban ababen more rayuwa idan aka zaɓe shi a shekarar 2027.
Ombugadu ya bayyana hakan ne a ƙaramar hukumar Awe yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe na ƙananan hukumomin jam’iyyar PDP gabanin babban zaɓe na 2027.
A cewarsa, tsaro zai kasance babban abin da gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali a kai, yana mai cewa al’ummar Jihar Nasarawa, waɗanda galibinsu manoma ne, dole ne su samu damar zuwa gonakinsu, su yi barci cikin kwanciyar hankali, su kuma gudanar da harkokinsu ba tare da tsoro ba.
Ya yi alƙawarin gagarumin ci gaban ababen more rayuwa, da suka haɗa da gina tare da gyara hanyoyi domin haɗa al’ummomi da bunƙasa harkokin tattalin arziki.
Ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da an gina hanyoyin da suka haɗa Akiri da Filato da sauran muhimman hanyoyi, tare da haɗa jihohin Benue, Awe, Taraba da Filato domin tabbatar da hanyoyin sadarwa kai tsaye domin haɗin kai da kasuwanci.
“Za mu haɗa hanyoyi kamar Wuse zuwa Taraba da sauran mazaɓu domin buɗe karkara,” in ji shi.
Ombugadu ya kuma ce gwamnatinsa za ta inganta yawon buɗe ido na cikin gida a matsayin hanyar samun kuɗin shiga, inda ya ambaci bukin kamun kifi na Hunkuyi da ruwan zafi na Awe, wanda ya yi alƙawarin bunƙasa domin tallafawa al’ummomin da ke ɗaukan baƙuncin.
Ya sake tabbatar wa al’ummar Awe da jihar baki ɗaya cewa dukkan tsare-tsaren da alƙawuran da ya yi a 2019 da 2023, da waɗanda ake yi gabanin 2027, za a aiwatar da su.
“Ba zan baku kunya ba,” ya tabbatar.
Tun da farko, shugaban jam’iyyar PDP na Jihar, Dakta Daniel Gimba, ya ce ƙaddamarwar ta nuna ƙudurin jam’iyyar na fita daga cikin wahalhalu da kuma gabatar da shugaba na gaskiya wanda zai kai jihar ga tudun mun tsira.
Gimba ya bayyana Ombugadu a matsayin mutum mai gaskiya, riƙon amana da kuma ƙwazo, yana mai nuna ƙwarin gwiwar cewa PDP za ta yi nasara matuƙa idan ba a tafka maguɗi a zaɓen ba.
Ya ce tutar jam’iyyar da aka ba ‘yan takara alama ce ta tafiyarsu da kuma umarni na yin nasara a yankunansu na Sanata, mazaɓu da jihar baki ɗaya.
“Yau rana ce mai cike da tarihi da muhimmanci. Mun zaɓi fara rangadin ƙananan hukumominmu, wanda ke nuna nasararmu mai zuwa a 2027 da yardar Allah. 2027, babu ja da baya,” in ji Gimba.
Haka kuma da yake jawabi a madadin sauran ‘yan takara, ɗan takarar Sanata na Nasarawa ta Kudu na PDP, Dakta Mike Omeri, ya gode wa magoya baya da mambobin jam’iyyar bisa amincewa da suka nuna musu.
“Tare da ku, za mu yi yaƙin neman zaɓe domin mu yi nasara, kuma za mu lashe wannan zabe,” in ji Omeri.
A nasa ɓangaren, Mukaddashin shugaban majalisar yaƙin neman zaɓen PDP, Mista Mark Ogbole, ya ce jam’iyyar ta zabo Awe da gangan domin fara yaƙin neman zaɓe na lumana ga jihar baki ɗaya.
Ya yi alƙawarin cewa gwamnatin PDP za ta samar da ayyukan yi ga matasa tare da tallafawa mata da jari domin inganta rayuwar iyalansu, yana mai cewa jam’iyyar na neman zaɓe ba don ta gudu bayan nasara ba, sai don ta yi wa al’ummar jihar aiki.
