Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Ɗan takarar gwamnan jihar Nasarawa a ƙarƙashin jam’iyyar APC Sanata Ahmed Aliyu Wadada ya samu cikakken goyon baya daga wata ƙungiyar siyasa ta ƙabilar Agatu da ake kira “Agatu United for Wadada 2027” gabanin zaɓen gwamna na 2027 a jihar.
Taron gangamin nuna goyon bayan da aka gudanar a Lafiya ya samu halartar manyan ‘yan jam’iyyar APC da jami’an gwamnati da sarakunan gargajiya domin nuna goyon baya ga burin Wadada ya karɓi mulki daga gwamna Abdullahi Sule.
Ƙungiyar ta Agatu United for Wadada 2027 ta ƙaddamar da sabbin shugabanninta a yayin taron kuma ta yi alƙawarin yin aikin tura mutane a dukkan al’ummomin Agatu a kananan hukumomin jihar gabanin zaɓen 2027 domin nasarar sanata Wadada.
Da yake jawabi a wajen taron sanata Ahmed Wadada ya shaida wa jama’ar da suka taru cewa siyasa ya kamata ta kasance kan shawo kan matsalolin mutane da abin da aka yi ba da tashin hankali ko zagi ba.
“Muna da abin da za mu bayar. Mun bayar. Muna da abin magana. Muna da shaida. Ina da jerin abin da Allah ya ba ni ikon yi,” inji shi.
Sanatan mai wakiltar Nasarawa ta Yamma yace tarihin sa na shekaru biyu a majalisar wakilai da kuma yanzu a matsayin sanata ya bambanta shi da sauran ‘yan takaran.
Wadada ya kuma sanar da bai wa ƙungiyar mota da kuma tallafin Naira miliyan 10 domin taimaka wa wajen ayyukan nasu.
“Kada ku je ku ce musu su zaɓe ni ne kawai saboda ɗan uwanku ne. Kuce musu su zaɓe ni ne bisa aiki na da tarihin aiki na da abin da na gabatar,” inji shi.
Ya yi alƙawarin gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin lumana kuma zai ci gaba da “HEART Agenda ɗin sa da NEDS” na gwamnatin yanzu ta gwamna Abdullahi Sule.
“Namu zai zama cigaba da ƙarfafawa don haka kada ku ji tsoro. Babban burin mu shi ne mu cigaba da zama cikin lumana da wadata” inji shi.
A nasa ɓangaren kodinetan ƙungiyar ta Agatu United for Wadada 2027 Kwamared Godspower Ede yace goyon bayansu ga Sanata Wadada ya samo asali ne daga dangantaka da kuma kwarewarsa a duka matakin rayuwa.
“Sanata Ahmed Wadada jikanmu ne. Mahaifiyarsa wato mama Iyatu Allah ya jikanta Agatu ce ta kabila. Wannan dangantakar jini tare da tarihin hidimarsa ne ya sa muka yanke shawarar goyon bayansa,” inji Ede.
Ede yace ƙungiyar ta mamaye dukkan al’ummomin Agatu a ƙananan hukumomin Doma da Nasarawa da Toto da kuma ta na da mambobi a ƙananan hukumomi 13 na jihar baki ɗaya.
Ya bayyana cewa za su kai gangamin kan wuraren zaɓe 127 a cikin al’ummomin Agatu 102 kuma sun buƙaci tallafin kayan aiki domin aiwatar da hakan.
“Dabarar mu za ta kasance kan tura mutane daga tushe da kuma ba da taimako kai tsaye daga ƙauyuka zuwa wuraren zaɓe inda ake lashe zabe,” inji shi.
Mai wakiltar gwamna Abdullahi Sule a wajen wato sakataren dindindin na harkokin majalisa a ofishin sakataren gwamnatin jihar ta Nasarawa Alh. Mohammed Iliyasu-Idde ya yaba wa ƙungiyar bisa inganta haɗin kai.
“Wannan taro ba wai na siyasa kaɗai ba ne yana nuna haɗin kan ‘yan uwantaka da jituwa da kuma ƙudurin ganin cigaba da cigaban jihar mu ,” inji shi.
Ya buƙaci mutanen Agatu da su cigaba da goyon bayan APC da zaman lafiya kuma su yi aiki don nasarar sanata Wadada.
Shi ma shugaban jam’iyyar APC na Jihar Dr. Aliyu Bello ya bayyana Wadada a matsayin wanda ya cancanta ya mulki Nasarawa inda ya ambaci rawar da ya taka wajen samun amincewa da kafa asibitin koyarwa na jami’ar tarayya a Lafiya da sauran su.
“Wadada shi ne ya ciyar da doki, shi ne kuma zai nuna wa dokin inda zai tafi. Ina ba da shawara cewa kuna da ɗan ku kuna da nama da wuƙa da tebur ku yanke shi yadda kuke so ku yanke,” inji shi.
Mataimakin gwamnan jihar a nasa jawabin wato Dr Emmanuel Akabe wanda Mr. Safiyanu Ogah ya wakilce shi yace Wadada “kaya ne da za a iya sayarwa” inda yace ayyukansa suna bayyane kana ya buƙaci a fito ƙwai da kwarkwata a zaɓe shi.
Abubuwa da aka gudanar a yayin taron sun haɗa da kaddamarwar da sabbin shugabannin ƙungiyar Agatu United for Wadada 2027 ɗin ƙarƙashin jagorancin Godspower Ede da sauran su.
