2027: Sarkin Ilorin ya yi wa gwamna AbdulRazaƙ da APC addu’ar nasara

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Sarkin Ilorin, Dakta Ibrahim Sulu-Gambari, ya yi wa ɗan takarar gwamna da sauran ‘yan takarar Jam’iyyar APC da Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaƙ, ke marawa baya addu’ar samun nasara a babban zaɓen shekarar 2027.

Sarkin ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a fadarsa, lokacin da dubban shugabanni da magoya bayan APC daga sassa daban-daban na Jihar Kwara suka kai masa ziyara domin gabatar masa da ‘yan takarar jam’iyyar tare da neman albarkarsa.

Tawagar ta samu jagorancin Shugaban APC na Jihar Kwara, Prince Sunday Fagbemi, kuma ta haɗa da manyan jiga-jigan jam’iyyar da dukkan ‘yan takarar APC. Daga cikinsu akwai Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kwara kuma ɗan takarar gwamna na jam’iyyar, Rt. Hon. Yakubu Salihu Danladi, da ‘yan takarar Sanata, na Majalisar Wakilai, da kuma ‘yan takarar Majalisar Dokokin Jiha daga faɗin jihar.

Da yake jawabi ga tawagar, Sarkin Ilorin ya ce ya yi matuƙar farin ciki da irin ɗimbin mutanen da suka halarci ziyarar, inda ya bayyana Gwamna AbdulRahman AbdulRazaƙ a matsayin shugaba mai nagarta da kuma kyawawan ayyukan ci gaba.

Ya yaba da shirye-shiryen ci gaban da gwamnan ya aiwatar a jihar, tare da yi masa addu’ar Allah Ya ƙara masa nasara a jagoranci, sannan Ya ba jam’iyyar APC nasara a zaɓen shekara mai zuwa.

“Tun da safe harabar fadata ta cika da magoya bayanku. Shin yau ce ranar zaɓe ne ko kuwa ziyara ce kawai kuka zo yi? Ina roƙon Allah Ya sanya albarka a duk matakan da Sadauna Ngeri (Gwamna) yake ɗauka,” inji Sarkin.

Sarkin ya kuma ce duk wanda ya ga alheri amma ya ƙi yaba masa, ba mutum ne mai gaskiya ba.

“Duk wanda ya ga abin kirki amma ya ƙi faɗarsa, mutum ne marar gaskiya kuma mai mugunta. ƙarya ba ta da wurin ɓoyewa. Mu faɗi gaskiya kamar yadda take. Abin da muke gani a ƙasa gaskiya ne. Duk wanda ya yi aiki nagari, ya kamata a yaba masa. Gwamnan ya yi aiki sosai,” inji shi.

By ukarofi

Leave a Reply