2027: Shugaban APC na Ƙasa ya sake ganawa da Sanata Kabiru Gaya

Spread the love

Tsohon Sanatan Kano ta Kudu, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, ya ganawar sirri da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, a gidansa da ke Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa, ganawar ta ɗauki kusan mintina 45, inda aka tattauna kan batutuwan siyasa da kuma makomar jam’iyyar APC a Jihar Kano.

Wasu majiyoyi sun yi ikirarin cewa Sanata Gaya ya nuna aniyarsa ta komawa jam’iyyar APC, duk da cewa har yanzu babu wata sanarwa daga gare shi da ta tabbatar da hakan a hukumance.

A nasa ɓangaren, shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya tabbatar da cewa ya karɓi baƙuncin Sanata Gaya, yana mai cewa sun tattauna cikin girmamawa da fahimtar juna kan muhimmancin haɗin kai da ci gaban siyasar Jihar Kano.

Wannan na zuwa ne bayan rahotannin da suka ce Sanata Gaya bai samu tikitin takarar Sanatan Kano ta Kudu a jam’iyyar NDC ba, bayan sauya sheƙa daga APC zuwa ADC, sannan daga bisani ya koma NDC.

Sanata Kabiru Gaya ya taɓa zama gwamnan Kano tsakanin 1992 da 1993, sannan ya wakilci Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
A zaɓen 2023, ya rasa kujerarsa bayan da Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila ya kayar da shi.

Sai dai, har zuwa yanzu, babu wata sanarwa a hukumance daga Sanata Kabiru Gaya da ke tabbatar da cewa ya koma jam’iyyar APC. Don haka, ana ci gaba da jiran matsayinsa na ƙarshe kan wannan batu.

By Babaji

Leave a Reply