2027: Wike ya gargaɗi PDP kan bai wa Arewa takarar shugaban ƙasa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan babban birnin tarayyar Nijeriya, Nyesom Wike ya ce ya ja hankalin Jam’iyyar PDP kan yunƙurin miƙa takarar shugabancin Nijeriya a zaɓen 2027 ga yankin arewacin ƙasar.

Nyesom ya yi gargaɗin ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai ranar Litinin, inda ya ce “me zai hana a matsayinta na jam’iyya ta fito fili ta ce ɗantakarar shugabancin ƙasarmu na 2027 zai fito daga kudanci?

“Ba sa son su yi hakan. Sun fi son su yi irin abin da suka yi a 2023. Tsarin ba zai je ko’ina ba. Wannan wayon ba zai kai ku ko’ina ba. Ku fito fili ku shaida wa duniya inda kuka dosa. Ba zai yi wu kai takarar zuwa arewa ba. Na faɗa musu. Son rai zai iya kashe kowane irin tsari.

Misali, idan shugaban ƙasa ya tsaya takara kuma ya samu nasara a zaɓen 2027, to a 2031 APC za ta mayar da takarar arewa ne,” inji Nyeson Wike.

By ukarofi