Majalisar ƙolin Shari’ar Musulunci ta naɗa Sheikh Isa Akindele a matsayin mataimaki

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar ƙoli ta Shari’ah a Nijeriya (SCSN) ta sanar da naɗin malamin nan mazaunin Ibadan Sheikh Isa Akindele a matsayin sabon mataimakin shugaba na ƙasa.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da kwanan watan Mayu 11, 2025, kuma mai ɗauke da sa hannun Nafiu Baba-Ahmad, mni, Sakatare Janar na (SCSN), amma Manhaja ta samu a ranar Talata, 13 ga Mayu, 2025.

Sanarwar ta ce; “Bayan shawarwarin da suka dace kuma bisa tanadin kundin tsarin mulkin Majalisar Koli ta Shari’ah a Nijeriya (SCSN), Majalisar ash-Shura ta Majalisar ta sanar da zaɓen Sheikh Isa Akindele a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar Koli ta Shari’ah a Nijeriya.

“Wannan naɗin ya zo ne bayan rasuwar tsohon Shugaban Majalisar, Sheikh Abdur Rasheed Hadiyyatullah (Rahimahullah), da kuma tabbatar da Sheikh Dr. Bashir Aliyu Umar, OON, a matsayin sabon Shugaban Majalisar ƙoli ta Shari’ah a Nijeriya.

“A bisa tsarin sake fasalin shugabancin majalisar da kuma tabbatar da ci gaba da ƙarfafa a ayyukanta, an naɗa Sheikh Isa Akindele a matsayin mataimakin shugaba na ƙasa bayan da aka yi la’akari da zurfin iliminsa na Shari’a, da tsayin daka wajen gudanar da da’awa, da kuma sadaukar da kai ga al’ummar Musulmi a Nijeriya.

“Majalisar ash-Shura tana kira ga ɗaukacin mambobin majalisar, ƙungiyoyi masu alaƙa, da sauran al’ummar Musulmi da su ba da cikakken goyon baya da haɗin kai ga sabon shugaban.

“Muna addu’ar Allah (SWT) ya ƙarawa Sheikh Isa Akindele da ɗaukacin tawagar shugabanni hikima da ikhlasi da nasara wajen gudanar da ayyukansu domin daukaka addinin Musulunci da hidimar al’umma.”

Kamfanin Dillancin Labaran iƙna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa ta Manhaja cewa, kwanaki biyu bayan rasuwar Sheikh Hadiyatullahi, majalisar shari’ar musulunci a ranar 30 ga watan Afrilun shekarar 2025 ta sanar da nada Sheikh Dr. Bashir Aliyu Umar a matsayin sabon shugabanta.

Sheikh Umar wanda ya taɓa zama mataimakin shugaban majalisar, fitaccen mutum ne a fannin ilimin addinin Musulunci da kuma harkokin kudi a Nijeriya.

Yana da Ph.D. Ya karanta Hadisi da Ilimin Addinin Musulunci daga Jami’ar Musulunci ta Madina kuma ya yi aiki a kwamitoci daban-daban da suka shafi Shari’a da Bankin Musulunci a Nijeriya da ma ƙasashen duniya ciki har da Kwamitin Shawarwari na Shari’ah na Bankin Stanbic IBTC da Majalisar ƙwararru kan Bankin Musulunci na Babban Bankin Nijeriya (CBN).

By ukarofi