Daga UNCLE LARABI
Ina mamakin yadda kuke kasa amfani da tunaninku wajen gane cewar, da Tinubu da Peter Obi duk abu ɗaya ne, kawai shi Tinubu ya yaudare ku da Musulunci ne. Sannan shi Atiku ko ya ci kujerar Shugaban ƙasa babu abin da zai canja daga irin mulkinsu Tinubu ɗin.
Shi Tinubu ana so a kawar da shi a kawo wani sabo ne, don a koya wa duk wani shugaba darasi. Da a ce a 2019 ba a sake zaɓen Buhari ba, an kifar da shi da ko waye ya hau bayansa, sai ya shiga taitayinsa, amma sai ’yan Arewa masu son zuciya da kishin addini na ƙarya suke cewa ai gara Buhari ya zarce da Atiku.
Peter Obi yadda ya ba wa ’yan Arewa wahala haka Tinubu ya ba wa ’yan Arewa wahala a Lagos. Tinubu yana ado da Musulunci ne, amma ba wani cikakken Musulmi ba ne. Sannan Musulmai nawa ne suka yi mulki a Nijeriya ɗin ba su yi komai ba banda wahala da suka gadarwa ƙasar?
Yanzu fa duk neman da muke ciki ne yake cinyewa. Masu ƙoƙarin hawa mota, don kada a ce sun talauce sai fetur ya ƙara kwasar wani kason.
A dalilin Tinubu da mulkin zaluncinsa yanzu babu wani abu mai sauƙi. Hatta kasuwancinmu kowa ya san ya ja baya tunda fetur na tsada matan ma ba koyaushe suke fito wa kasuwa ba, saboda tsadar kuɗin Adaidaita Sahu (Napep). Don haka ku canja tunani.
2027 zaɓe ne tsakanin masu hankali da masu ƙarancin tunina. Ko dai a tsaya a kifar da Tinubu a kawo sabo. Shi ma idan bai yi komai ba a shekara huɗu a kifar da shi a kawo wani sabon. Idan sun ga ana yi musu haka a hankali za su gyara.
Larabi, wato Abdullahi Jibril Dankantoma, za a iya samun sa a 08065418892
Jihar Kano – Nijeriya
11 ga Mayu, 2026
