Ba a san inda Obaseki ya ke ba, inji gwamnan Edo mai jiran gado

Daga BELLO A. BABAJI

Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo ya bayyana damuwa kan yadda ba a san inda Gwamna mai barin gado, Godwin Obaseki ya ke ba, ya na mai cewa ya ajiye harkar shugabanci a jihar.

Cikin wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Godspower Inegbe, Okpebholo ya ce al’ummar Edo sun damu game da kalaman Obaseki masu tunzurawa, ya na mai kiran sa da kama kansa.

Okpebholo ya bayyana cewa Obaseki ya yi basaja ne cikin wata mota ƙirar Bus inda ya fice daga Benin, babban birnin jihar wanda gabannin haka da kwana uku, ya kori baki ɗaya mutanen da ke gidan gwamnatin jihar.

Takardar ta kuma ce, Obaseki ya yi hakan ne a ƙoƙarinsa na ficerwa daga ƙasar da hanyoyin kan iyakan ƙasa.

Zaɓaɓɓen gwamnan ya ƙara da cewa, hakan wani yunƙuri ne na ƙoƙari sauya hukuncin ƙarar da aka shigar akan sa ta hanyar amfani da zantukan ƙarairayi.