Amurka: Biden ya ayyana ranar da zai gana da Trump

Ppppppp BELLO A. BABAJI

Shugaban ƙasar Amurka mai barin gado, Joe Biden zai gana da zaɓaɓɓen Shugaban ƙasa, Donald Trump a ‘White House’, a ranar Laraba, 13 ga watan Nuwamba bayan Biden ya amince da miƙa masa mulki bisa tsari jim-kaɗan bayan nasarar da ɗan takarar jam’iyyar ta Republican ya samu.

Za su gana ne da misalin ƙarfe 11 na safe a offishin Oval da ke Fadar gwamnatin ƙasar yayin da Trump ke shirin koma wa karagar mulki a karo na biyu.

A ranar 5 ga wata ne Trump ya sake lashe zaɓen ƙasar da rata mai yawa duk da bututuwan laifukan sata akan sa, da tsige shi da aka taɓa yi har sau biyu a lokacin da ya ke shugaba da kuma gargaɗi daga tsohon shugaban ma’aikatansa kan ƙalubalantar sa da wasu laifuka.

Ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen sun nuna yadda ƴan ƙasar suka damu da yanayin tattali da hauhawar farashi a ƙarƙashin jagorancin Biden musamman bayan aukuwar annobar COVID-19.

Kasancewar Biden mai shekaru 81 ya zaɓi janye tsayawa takara, ya sa mataimakiyarsa Kamal Harris ta maye gurbinsa.

Ya kuma taya Trump murna bayan lashe zaɓen nasa.