Masu zanga-zanga da aka saki sun musanta zargin cin zarafin su a hannun DSS

Wasu mutum biyu da aka kama a lokacin zanga-zangar ƙuncin rayuwa sun bayyana cewa ba a ci zarafin su ba yayin da suke tsare a wajen hukumar DSS.

A cewar su, an sake su tun watan da ya gabata daga ofishin hukumar DSS da ke Kaduna. Sun tabbatar cewa babu su cikin waɗanda aka kai Abuja kuma a ka gurfanar gaban kotu.
Su biyun sun kasance DJ suke yi yayin zanga-zangar wanda shine ya sa aka kama su.

Ɗaya daga cikin su, Isa Abdullahi ya musanta zargin cin zarafi a lokacin da yake tsare a ofishin hukumar, ya bayyana cewa an barshi yayi waya da matarsa a lokacin da yake tsare.

Ya cigaba da bayyana cewa duk da haka an basu kulawa da musamman. Isa ya jinjinawa shugaban hukumar da ya bada umarnin a sake ba tare da wani tuhuma ba.

Ɗaya daga cikinsu, Ɗahiru wanda mazaunin Tudun Wada ne a kaduna, shima ya yabawa shugaban hukumar da ya bada umarnin sakin su bayan ya fahimci cewa basu da wani laifi.